A'a. Husufin Farin Ciki ba littafi ba ne kamar yadda kuke zato — kuka zata. Husufin Farin Ciki ya wuce nan. Matattarar shauƙin bil'adama ne, mafakar ruhikan da suka raunata ne, soron matafiyan da suka rasa guzirin tafiya ne. Gida ne. A'a, ƙasa ce, da ta ƙunshi duk wani al'amurai da ɗan Adam ya taɓa wassafawa a zuciyarsa. Husufin Farin Ciki wani shinge ne da ba a tambayar kyawu ko rashin kyawu, mai ya kamata ko akasinsa. Ba a ma sansu ba ballantana a bambance su. Shigifa ce da duk wanda ya ratsa ta cikinta zai fito mutum kamallale - kamar aƙili, kamar majnuni. Ba wai ana wa mai karatu alkawarin aminci ko nutsuwar zuci ba ne. Ko kusa. Ta yaya za ka riski aminci ba tare da zuciyar ka ta ɗan ragargaje ba. Ta tubure. Ta ɗan haukace ba? To Husufin Farin Ciki hanya ce dan tabbatar da hakan. Tabbas za ka riski abin da kake muradi. Amma...
Amma kuma sai ya kasance mutum zai iya riskar duk abubuwan da aka lasafta a wata dunƙulalliyar takarda. Shin sai mu kira shi da littafi? Ina! Ya wuce nan. Amma dai littafin ne. Ko-ko nace, dole na yi nazarinsa a mahangar littafi.
Husufin Farin Ciki diwanin gajerun labarai ne da ke ratsa zuciyoyi tare da tayar da wani irin shauƙin da ba lallai an san da su ba. Labaran na rikiɗewa a yayin da ake karantasu, sai su zama zuma ko maɗaci. Wani zubin kuma sai su gwaraya. Wani zubin ko ka ma gaza bambantasu. Labaran, har wayau, na da ɗanɗano daban-daban. Amma dukansu sun yi tarayya a abu guda. Wato ɗanɗanon ruwa gare su. I, ruwa ba shi da ɗanɗano amma ai wasu ruwan na da. Wasu lokutan sai mutum ya fara jin ɗanɗanon gishiri wasu lokutan kuma sai labaran su zama kamar ruwan dai. Kamar ruwan sha; marar ɗanɗano; marar ƙamshi. Ɗanɗanon gishiri dai na kama da ruwan teku. Kuma gishiri ma sinadarin hawaye da hauhawar zuci ne. Akwai gishiri a teku sannan akwai shi a ruwan hawaye. Sai dai kuma ba iya ɗanɗanon da mutum zai ji ba kenan. A farko ma ba lallai ya ji komai ba, Kamar dai ruwa. Daga bisani sai ruwan ya rikiɗe ya zama mai gishiri-gishiri. Teku-teku. Kamar dai ruwa, kamar teku.
Wasu labaran kam an masu ado ne da alkyabba mai duhun launi. Kamar dai duhun kafin fitowar alfijiri. Wannan alkyabba kuwa tuni yake yi wa makaranta kan: soyayya, ƙauna, bege, rashi, takaici, kewa, rashin rabo, samu, farin ciki, baƙin ciki, jan ciki, harma da ƙoriyar ciki!
Wani abun yabawa game da littafin shine yadda a duk sanda mutum zai karanta shi — koda ya taɓa karantawa — zai ji kamar bai ma taɓa karantawa ba. Shauƙin na canzawa ne a koda yaushe. Kamar yadda dai Zuciyar ɗan Adam yake. A kullum labaran sababbi suke ga makarantansu. Wannan ko ba zai rasa nasaba da sana'ar marubucin ba — Tsafi. Ƙasurgumin matsafi ne. Ya ƙware wajen dabo da kalamai har ma ya busa masu rai. Ya zamana muna ganin su a yayin da muke karanta su. A zahiri kaɗai ne a ke karantawa, a baɗini kam mu ne a labaran muna kallon komai yana gudana a gabanmu. Ba iya busa wa kalamai rai ya yi ba, har shauƙi ya sanya musu. Abin da masana kimiya suka kasa yi, shi wannan BaKanon ya yi da ƴar takarda da alƙalami!
Wasu labarai ne haka nake ta koɗawa? Kun ma san su, kun taɓa jin su, kun taɓa riskar su. Amma akasarin mutane na kauda kai ga irin waɗannan labaran, ba sa so sam su tuna da su. Mun fi son a kullum mu yi ta rayuwa cikin farin ciki. Babu mai son farin ciki ta yi husufi, to amma kuma ta na yi, a kullum. A kullum labaran duniyar nan dai tamu na da nasu kalar husufin. A layin mu, a unguwar mu, a ƙasar mu. Wannan matsafin ya yi ƙoƙarin kawo mana labaran da ba mu cika son magana akai ba, da wasu kuma waɗanda muka kasance masu kau da kai a kan su. Sai ya hasko mana su, ya nuna mana su, ƙarara
.
Labaran dai sun fi ashirin amma babu waɗanda suka fi ƙayatar da ni sosai kamar: Husufin Farin Ciki, Akwatin Gidan Waya, Dama Dai A Ce, Duniya Labari, Bala da Hannatu, da Tangaraho. Ba wai duka sauran ba su yi bane, ko kusa, duk wanda ya karanta abin da na rubuta a baya ya san dukansu sun yi ainun. Waɗannan ne dai zan ɗan yi tsokaci kaɗan akai domin waɗanda ba su taɓa karantawa ba su ɗan gane mai ya sa nake ta koɗa wannan ‘littafi’.
Labaran dai sun fi ashirin amma babu waɗanda suka fi ƙayatar da ni sosai kamar: Husufin Farin Ciki, Akwatin Gidan Waya, Dama Dai A Ce, Duniya Labari, Bala da Hannatu, da Tangaraho. Ba wai duka sauran ba su yi bane, ko kusa, duk wanda ya karanta abin da na rubuta a baya ya san dukansu sun yi ainun. Waɗannan ne dai zan ɗan yi tsokaci kaɗan akai domin waɗanda ba su taɓa karantawa ba su ɗan gane mai ya sa nake ta koɗa wannan ‘littafi’.
Husufin Farin Ciki dai labari ne a cikin Husufin Farin Ciki. Wannan labarin kam ya ci sunansa, domin tun a farko mai karatu zai fara ganin alamar husufi a gajimaren labarin, yana ɗan tuttuɗowa, a hankali. Labarin gabaki ɗaya an rubuta sa ne da alƙalamin rashi mai kama da na kewa, abin mamaki kuwa a kan takardar farin ciki a ka zana labarin (haka nake tunani). Sai dai a lokacin da ake zaton “Husufin Farin Cikin” ya game labarin sai, a hankali, rana ta bayyana, tare da haska labarin, kamar dai yadda take yi wa mazauna duniya. Ai husufi na ɗan ƙanƙanin lokaci ne, zai iya ɗaukar daƙiƙu, mintuna, har shekaru ɗari ma, amma kuma za mu iya neman ranar mu idan muna so. Za mu iya riskar ta, duk da dai alamu ya nuna ta ɓoye ne ba bisa rayin ta ba. “Shin za mu sake samun haihuwa?” Alhaji Ngidda ke nan ke tambayar matarsa jim kaɗan bayan ziyarar husufi.
Dama Dai A Ce labari ne da ke nuna yanayin al'ummarmu, musamman ta wajen bambance-bambancen mazauna cikinta. Yadda duwatsu suka bambanta; wasu manya, wasu ƙanana; wasu mahaskaka; wasu masu duhu. Yadda ƴan yatsun hannaye suka bambanta a tsayi da yadda ma kaifin rana a duniya ta bambanta sashi-sashi, haka mutanen cikinta suka bambanta. Akwai wasu mutanen da za mu so mu yi tarayya da su, ko da na ƙanƙanin lokaci ne, sai dai kuma idan muka yi duba da abin da ka iya zuwa ya dawo sai mu sauka daga wannan nufi tamu. Ba wai don ba ma son kasancewa tare da su ba ne, sai dai akwai wani abu da muka hango wanda zai iya hana mu aminci nan gaba. Walau ta ita kanta al'ummar mu, ko dai mu karan-kan-mu. Akwai mutanen da zamu so su ainun, amma idan muka yi nazari kan su sai mu ga ba mu dace da su ba. Ba mu ma cancanta da wannan son ba. Sun ɗare mana. Galibi ɗan Adam na kallon duniyar ne da tasa mahangar, kuma ta hakan yake wa duniyar fassara. Amma ita ma duniyar tana kallon kanta ta wata sigar da ba lallai ne mu kula ba. Wannan labarin furen so ne da ke bisa kan bishiyar da hannayenmu ba za su taɓa kaiwa ba. Sai dai zuciyoyin mu su kalla, su adana ta a can wata ƙurya tare da binne ta. Ba tsoro ba ne, a'a, ƙololuwar soyayya ce!
Bala da Hannatu kuwa mafi gajartar labaran ne. Labari ne wanda muke riskar makamancin sa a rayuwar mu na yau da kullum a wannan sashe na duniyar tamu. Abin da ya fi ƙayatarwa a labarin shi ne gajartar saƙonsa. Kamar dai yadda na ambata ne a baya, cewa mun kasance masu kau da kai ga abubuwa da dama a al'ummar mu. Amma hakan ba shine zai sa matsalar ta kau ba, hakan ma daɗa kambamata yake. Matsalar ta yi ta faɗi da girma a yayin da muka ci gaba da kau da kawunanmu. Rabuwa mai kama da kamuwa; Ba ta da wuri, ba ta da takamaiman lokaci, ba ta da sifa. Faruwa kawai take. Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kuma. Hannatu ta biɗi Bala da ya sake ta, shi ma ya buɗa bakinsa ya sake ta. Shi ke nan, wannan shafin ya kau. Idan da damar buɗe wani shafin za a yi daga baya. Ƙila Hannatu ta dawo gida ta yi zawarci, ƙila iyayenta su koro ta gida, ƙila su ce mata idan ta bar gidan kar ta dawo gidansu, ƙila ma sun daɗe da tsinke igiyoyin auren, ƙila su zauna a tare a hakan, duk saboda mun kasance al'ummar da ba ta ƙoƙarin warware zarurrukan matsalolinmu, sai dai mu binne matsalar a turɓaya marar ƙarfi, ƙarshe dai matsalolinmu su ci gaba da yaɗuwa ba tare da an magance kowanne ba. Magana mai inganci tare da yin huɓɓasa, a lokacin da ya dace, na iya gyara kaso mai tsoka daga matsalolinmu. Amma ba ma yin hakan a lokacin da ya dace, sai a ƙurarren lokaci, bayan aikin gama ya riga da ya gama.
Duniya labari, labari ne da ya ɗarsu a zuciyata ya yi min naso. Kamar dai ni ne kowa a ciki kuma kowa ma ni ne. Musamman ga waɗanda suke bibiyar tarihi, irin waɗannan labarai kusan na ko'ina, amma kuma dai a siffar tarihin suke. “Shin wane yare ne kai?” Da a wata sashen duniyar muke da sai mu ce na magabatanmu. Amma a wannan sashen, ba zamu iya faɗar haka ba, domin babu tabaccin cewa daidai muke faɗa. Labarin dai ya ba mu amsar wannan da cewa: “Yare na ne ni.” ”Yare na shine yaren da na tsinci kaina a ciki”. Ba kasafai ake samun irin waɗannan labarai ba a duniyar adabin Hausa. Ƙagaggen Tarihi salo ne da ba kowa ne ke yi ba, saboda yawan binciken da ke tattare da shi. Saboda haka dole a yaba wa wannan marubuci da ya yi ƙoƙarin raya wannan salo na rubutu da ya ke a kushewar adabin Hausa. Labari ne da ya taɓa zamantakewar ƙabilun ƙasar Hausa ta fuskar auratayya, cuɗeɗeniya, narkewa, da adadin zannuwan asali. Musamman yanzu da aka samu wasu masu nuna wane ne BaHausa a ƙasar Hausa, tare da fitar da wasu daga dausayin saboda wasu dalilai na su, wannan labari ya yi ƙoƙarin haska sarƙaƙiyar da ke tattare da asali a ƙasar Hausa ta salon da duk wani makarancin tarihi zai fahimta. Yanzu jikoki da tattaɓa-kunin Inda Musa Hausawa ne ko kuwa Nufawa? Shin sani na da tasiri a asali ko kuwa? Shin kakannin Inda Musa Nufawa ne ko wasu ƙabilun daban? Bayan ƙabilar kakanni, me ke da tasiri a kan asalin mutum? Amsoshin waɗannan tambayoyin na a ɓoye a cikin wannan labari. Idan kana so ka ga yadda ƙasar Hausa take a shekaru ɗari da suka gabata, sai ka zo ka yi iyo a tafkin wannan labari mai ƙamshin duniyar baya!
Akwatin Gidan Waya lula ni ya yi ya tafi da ni wata duniyar can daban, inda nake iya ganin rayuwa a lokaci mabanbanta. Al'adu a lokaci mabanbanta dama mu'amala a lokaci mabanbanta. Labari ne da ya nuna ƙwarewar marubucin a fagen tarihi. Sanin tarihi da iya amfani da shi a labari sai fasihi! Labari ne kan bege da kewa da ma wasu abubuwan.
Tangaraho labarin soyayya ne; labarin rashi ne; labarin samu ne; labarin zunubi ne; labarin lada ne; labarin ƙauna ne; labarin kewa ne. Labari ne da ba lallai a kuma samun irin sa ba. Kowane harafi, kalma, aya, waƙafi sun yi tarayya ne a waje ɗaya, domin isar da saƙo ɗaya - shiru. Labari ne da ya ginu a kan haka, tun daga farkon har ƙarshen. Shirun fa ba na rashin magana ba ne, ko kaɗan. Shirun da ke cikin ruhika ne aka bayyanar da shi. Irin shirun nan ne da ke sa zuciyoyi su zama kamar fanko, ba komai cikin su sai tsagwaron shiru. Irin wannan shirun ne ya kanannaɗe labarin, har ya kai mun fara ganin kawunanmu a labaran. Ni ne Hajara, ni ne Imrana, ni ne Tangaraho, Ni ce keken Imrana. Labari ne wanda, har wayau, husufi ya ƙwanƙwasa wa ƙofa, sai dai ba iya ƙofar sa ya ƙwanƙwasa ba, har da na ma su karanta shi. Ya samu nasarar ƙutsawa cikin kowane kalma da harafi. Ya yi abin da ya so, in da yaso, mu na so ko ba ma so. Sai dai, wannan Husufin bai zo da wuri ba amma ya wuce da wuri — kamar dai Husufin da aka yi shekarar da ta gabata a duniyar mu. Amma fa bai wuce haka ba, sai da ya bar ɓurbushinsa a iskar da muke shaƙa. Shi ya sa, a yayin da nake rubuta wannan sakin layin, na san na shaƙe sa, kuma iskar da ke ɗauke da shi zuciyata ta shiga. Ga ta can ta yi babakere a cikin zuciyata. Iskokin tangaraho ne suka aiko shi!
A dunƙule dai wannan littafi ya ci sunansa. Sannan marubucin ma ya ci sunansa. Sarrafa zantukan zuci zuwa rubutu sannan a kuma sarrafa su zuwa ababe masu shauƙi, babu shakka sai fasihi. Faɗar abubuwan da muke kauda kai tare da zayyana su ta salo mai ƙayatarwa wani abun a yaba ne. Tabbas marubucin ya ci sunansa. Matsafi ne. Domin ga shi dai duk da na yi nisa da littafin, ga ni a wata duniyar da ya kamata na manta da komi, maimakon haka, na tsinci kaina ina mai tunawa da ham ɗin motar Zainal-Abideen. Ƙarar ham ɗin nake ji. Kuma ƙarar daga cikin zuciyata ne, ba fa ham ɗinsa na farko ba, na ƙarshe. Ham ɗin bankwana.
20/02/25
Alhassan Maibasira
