Friday, 25 April 2025

Kukan Kurciya

Akwai wata kurciya da ke zuwa bakin tagata kullum da safiya. Kukanta mai daɗi ke tayar dani daga barci. Na kan kwashi lokaci mai tsayi ina kallonta, ina sauraran kukanta, ina mai ninkaya cikin duniyar mafarkaina wasu lokutan, har da mafarkanta— idan naci sa'a. A cikin duniyar tata mafarkai ne a jere da burika irin tasu ta dabbobi, kar ka tambaye ni wai ashe suna da mafarkai. Ca akai kai kaɗai ne mai iya yin su? 

Ƴar alkawari. Da hakan nake kiranta. Baiwar Allāh abar kwatance. A duniyar tata akwai ma'adanar rayuwarta ta baya. Nan na leƙa wata rana. Sai na ganni a wani kufayi; kango mai haske abin haskakawa. Na gano iyayen ta da ma ƴanuwanta su su duka a zaune. Bayani ne kan yadda rayuwarsu ta ke kasancewa a wannan duniyar. Mahaifin ne ke magana yanzu; baƙi, ƙaƙkaura, idanunsa ja tamkar na Hasbiya. Ya na riƙe da ƴar sanda, alamar tsufa. 

“Iyayen mu sun shaida mana cewa; an shaida wa iyayen su cewa; kakanninsu sun taɓa riskar wani zamani mai ƙayatarwa. A lokacin babu injina ballantana motoci. Saboda haka akwai bishiyoyi da dama, inda ahalinmu ke rayuwa. Rayuwa ce mai sauki a lokacin; babu ƙara, babu datti, babu shara, babu kiɗa; sannan kuma akwai gida. A kowane lokaci suna iya komawa gida ba tare da sun shiga cikin taskar wasi-wasin kasancewar yana nan ko akasinsa ba. Lokacin fa ba a cire masu bishiyu ba bisa ka'ida ba. Kamar na taɓa jiyo kakana Alto yana cewa lokacin Hausawa ke mulkin ƙasar Hausa ba Fulani ba. Sai dai ban san takamaiman lokacin wani sarki ne ba. Ku faɗa mini yarana: shin rayuwa bata fi sauki a da ba. Yanzu ko da ba a cire bishiyoyin ba, ruwan saman mai ƙarfi da ake yi zai cire shi. Duk saboda halayyar bil'adaman dake zamanin mu.”.                                   

Sai mahaifiyar tai caraf ta ƙara da cewar: 

“Ai ko jiya sai da leda ta sarkafe ƙafafuwan Lami da taje farautar ƙwari. Da ƙyar na samu na iya cirewa. Kalli har yanzu da sauranta a cikin yatsunta. Har sai lokacin da Allah ya yi. Abin da ba su ma ganewa— wato su bil'adaman nan— shi ne: abubuwan nan sun ma fi cutar su. Jiya nake ji, a tagar Mallam Sani, wai ga-baki-ɗaya makwararar Jakara ta toshe, saboda haka, mazauna kusa da ita su kiyaye, kasancewar idan aka yi ruwa mai ƙarfi, za a iya ambaliya. Ko-ko ma zafin nan da ake ta zabgawa, ko mu nan da-ba-dan tsarin hallitar da Ubangiji Ya yi mana ba, ai da wani zancen ake. Kuma duk me yasa hakan? Rashin shuka bishiyoyin da za su ci karo, koma su daɗa, waɗanda ake cirewa, da wasu dalilan can.”

Babban ɗan, wanda ya kasance ma'abocin karance-karancen tarihi, sanye da ɗan madubinsa ya ƙara da cewa: “Kun ga kuwa rayuwa ta fi daɗi a lokacin baya. Ina-ma- ina-ma, zan iya komawa can. Na biye wa tawagar Sarkin Zazzau Muhamman Makau lokacin da aka ci ƙasar sa da yaƙi. Yana tafiya da tawagarsa ina biye masa, har su isa Abu-Ja. Nayi zamana a can. Ina ma a ce a wancan ƙarnin a ka haifemu! Ga bishiyu, ga tsaunika, ga ƙoramai, ga ruwa mai kyau. Rayuwa mai daɗi! Uwa uba, ga tsafta. Gari ƙal-ƙal sai kace Aljanna.”

Shin ya Aljanna take? Ka taɓa zuwa ne?” In ji kurciyata, wacce ta kasance a kishingiɗe a saman tsabar da ke kwance a kangon, kanta na kan fika-fikin mahaifiyarta. Sai na ga duka manyan sun ƙalƙale da dariya. Mahaifiyar ko ta janyo ta, ta lakaci hancinta da nata hancin cikin zallar so. 

Mahaifin ya yi gyarar murya ya na mai cewa: “lokaci ya yi, yanzu ina muka dosa?”. A daidai lokacin sai na jiyo ƙarar injin ‘rum-rum-rum’. Sai muka jiyo ‘dum!’ Mai ƙarfi. Na waiga, kafin na juyo kuma, sai na jiyo “Fap...fap...fap”...

Mahaifiya ke jan gora, mahaifin ke bayan ayarin, Ƴaƴayan na tsakiya. Tafiya suke kamar ba za su tafi ba . Da suka nisa sai duk suka juyo, suna masu kallon gidansu a ƙaro na ƙarshe. “Rrrr”— ƙara ya tsaya cak. Amma bishiyarsu— gidansu— babu. Sun tafi kenan. Har abadan... a-ba-da.

Da na dawo zahiriyya, sai na nitsa a cikin kogon tunani. Abubuwan da suka wakana tamkar a mafarki. Na yi mamaki ƙwarai da ba su lura dani ba. Wai shin ko na mutu ne?... Amma kuma wani abu guda daya kasance yana ta yi min kulumboto a cikin zuciyata; kamar na san wurin ko ma na taɓa rayuwa a inda na riske su. Kamar na san kangon nan. Kamar na san ginin nan. Kai, na ma san su! Da na nitsa sai na fahimci cewar, ai inda ma suke tsaye a nan ɗakina yake. Inda aka yi wa ƴaƴayan huɗuba ai a cikin gidan nan yake. Bishiyar da ma na tsakiyar kangon ne. 

Dabbobi ma, kamar ɗan Adam ba sa mance gida. Dabbar ma tsuntuwa. Tsuntsuwar ma Kurciya. Ashe, shi ya sa, a kullum take tashina daga barci. Kukan da take yi ai tuni take min, magana take min, wa'azi take yi min: “Duk inda halittar Ubangiji zai kai ya kawo ba za ya taɓa mantawa da gida ba. Nan ne gidanmu, ba zan iya mantawa da shi ba.”

Washegari na tashi a makare kasancewar ba ta zo ba. Mai tashina ba ta. Sati yazo ya wuce, wata ya rarrafa a sukwane, shekara ta zo a guje. Lokaci mai tsayi ya ja. Amma kullum da tunanin kurciyata nake tashi daga barci.

 “Baba, lokacin shan shayi yayi” na jiyo ɗan autana Sambo na faɗi. Na tashi, na shirya, na ishe su a ƙarƙashin bishiyar da na dasa shekarun baya— irin wacce na gani ne a mafarkin kurciyata. Kuma a inda na ganta a nan na kuma dasa ta. Ga kujeru, ga shayi, ga iyali, sannan ga Kurtattakina a saman bishiya, suna ta kukan su. “Kukan Kurciya dama ai jawabi ne.” ko ni ne na faɗa, ko Kurtattakin dake saman bishiyar ne, ba na ce ba.

MA. Maibasira

24/04/25





No comments:

Post a Comment

Da Kuma Akwai Wannan Lumanar Da Ba Za A Iya Fasalta Wa Ba

Da akwai wannan lumanar da bawa kan riska yayin da ya tsinci wannan littafin da ya yi shekaru yana nema a wata ƙurya a cikin ma'adanar t...