Saturday, 14 June 2025

Matafiyan Tsuntsaye


Akwai mutanen da suka kasance kamar tsuntsaye matafiya; sukan shigo rayuwar mutum lokaci guda — na lokaci ƙalilan. Kamar matafiyan tsuntsaye, sukan yi sheƙarsu a rayuwar mutum su yi ta rera masa waƙoƙi — su warkar da ciwukan zuciyar da ya addabe sa, su gyara masa rayuwarsa. Abubuwan da ba ya yi sai ya fara; idan ya faɗi su tayar da shi, idan ya kuskura hanya su dawo da shi bisa tafarki, idan ya nemi shagala su watsa masa ruwa don ya tashi. Idan ya nemi ya ɓata, su nuna masa hanya, duk ta hanyar waƙoƙinsu, waɗanda suke rerawa a kodayaushe. 

Kamar matafiyin tsuntsu, sai ya yi tafiyarsa ya bar sheƙar a saman bishiyar. Babu kowa dai a kai, amma a duk lokacin da mutum ya ɗaga kansa sama, zai hango gidan wannan tsuntsun da ya sauya masa rayuwa. Ba lallai ya kuma dawowa ba, ya tafi kenan. 

To haka Malam Jamilu ya zame wa rayuwata. A daidai lokacin da na gaza gane ina na dosa, sai ya yada zango a bisa bishiyata, ya yi ta rera mini waƙoƙin adabi, tarihi, da wasullan Hausa. Ya yi ta ciyar dani daga tsirran ƙasar Hausa. Idan na kishingiɗa ya taso ni, yace mini na je na nemo masa ciyayi domin mu tada baƙi. Neman ciyayi kam dama na bani wuya, amma duk da haka bai saduda ba. Akwai fa bishiyu da dama a wannan jejin, amma ni kaɗai ya horar fiye da misali. Ni kaɗai nake jin haka — kusan kowa yana sauraren waƙoƙinsa kuma yakan aike su domin su nemo ciyayin. 

A lokaci ƙalilan, bishiyata ta fara rassa, da kaɗan, da kaɗan furarruka suka fara fitowa. Sai dai an ɗau tsawon lokaci kafin bishiyar ta fara ƴaƴa. Lokacin ya bar shingen mu. Idan ma yana dajin baya kusa damu. Ni kuma saboda wautata sai na mance da shi, na ƙi na biɗesa. Na ƙi na tambayi ƙwari da tsutsosin da ke ƙarƙashin ƙasa ko sun taɓa ganinsa. 

Yau dai bishiyar ta fara ƴaƴa — haka nake tunani. To saidai, ashe ba zai taɓa riskar ƴar bishiyar da ya raina ba da kansa. Yar bishiyata da ya rera wa waƙe, ƴar bishiyar da ya zame wa fitila a cikin duhun dare. Yau ba zai gansu ba, yau ba zai taɓa dawowa bisansu ba. Ya tafi kenan, ashe ba zai kuma dawowa ba. 

Akwai mutanen da suka kasance kamar matafiyan tsuntsaye: sai su haskaka alƙaryar mutane da zatinsu, su yi ta shawagi a bisansu, su ƙayatar da duniyarsu. Sai kuma su tafi, za su dawo? Ƙila.... Wasunsu kuma sun tafi kenan. Sheƙarsu na nan dai, hakana tasirin su ga rayuwar mutanen alƙaryar. 

Irin waɗannan mutane ba sa mutuwa, ko sun mutu da akwai ɓurɓushinsu a jikin kowanne. Da akwai baitukan waƙoƙinsu a dashe a ƙalbin mutane. Da akwai ƙarin harshensu a bakunan mutane. Da akwai garɗin koyarwarsu a dasashi da ma saiwar bishiyoyi. Kogunan alƙaryar kam za su ci gaba da ɗaukar wasulla da baƙaken da suka taɓa suɗaɗowa daga waƙoƙinsu. Irin waɗannan mutane na rayuwa har abada. Irin waɗannan mutane ba sa mutuwa.

Allāh Ka gafarta wa bawanKa; Ya kasance kamar matafiyin tsuntsu ne a ban ƙasa. Kai ne Majiɓincinmu, Kai ne Mai rahama a garemu. RahamarKa ta baɗe ko'ina. RahamarKa na da tasiri akan kowa. Ka sanyaya masa yadda ya sanyaya mana. Ya yi iya nasa ƙoƙarin wajen kula da bayinKa; wajen ciyar da halittarKa; wajen ɗanɗana wa al'ummarKa daga ilimin da Ka tsam masa; Ka sa ya zama mai ƙwanƙwaɗa daga tafkin rahamarKa, don, koda ƴar ɗigo ya samu, ta wadace shi har abada. Allāh Ka gafarta wa Malam Jamilu, mutum ne salihu da bai son fitnu, ka buɗe masa ƙofofin rahamarKa, domin, ya kasance mutum ne mai kyawawan ɗabi'u.

Marigayi Malam Jamilu (d. June 2025)



Monday, 9 June 2025

Yawon Duniya

Masoyiya, shin za ki iya shimfiɗa 
Mini tabarma a wani sashe na 
Zuciyar ki don na zamna?
 
Ƙafufuwana sun gaji da 
Taku a cikin zuciyarki 
Babu dare, babu rana.

Ba lallai sai kin samo 
Kilishi ba ko kujerar 
Nan mai taushi da laushi.

Kawai soyayyarki nake so 
Ta zame mana tabarma; 
Ni a gefe ɗaya, ke a ɗaya.

Ta ja mu, ta ɗaga mu, ta lula mu:
Mu keta gajimare; mu ratsa ta 
Gangamin tattabaru; mu wuce sinadaran
Numfashi; mu lula mu tafi can inda cida 
Ke koyan tashi. Daga nan, ƙila, 
Sai mu garzaya duniyar taurari;
Mu faɗa kogin da ke bisansu, mui wanka, 
Mu sauya buƙatu, mu kaifafa muradai;
Mu tsaftace soyayyarmu.

A cikin zuciyarki, da zaki yarda, 
Da sai na janyo tabarmar nan bakin teku. 
Mu zamana muna kallon shirgawar 
Kifaye mu kadanmu 
Sai kuma teku.

Da zaki yarda, da sai na baza 
Komata don na kamo kifayen 
Da ke cikinai, kowannensu, na 
Buɗe cikinsu, inda ƙoƙon lu'ulu'u 
Mai ɗauke da soyayyarmu 
Ke ciki a ɓoye.

Masoyiya, so nake kawai na samu 
Aminci a cikin zuciyarki; ki ɗan lasa 
Mini daga tekun ƙaunarki; ki ci gaba 
Da alkinta mana soyayyarmu a cikin 
Ƙokon lu'ulu'u nan mai haske. 
Ƙila wataran, idan muka ƙare 
Yawon duniyar mu, zamu shiga 
Domin mu ga iya girmanta. 

Matafiyan Tsuntsaye

Akwai mutanen da suka kasance kamar tsuntsaye matafiya; sukan shigo rayuwar mutum lokaci guda — na lokaci ƙalilan. Kamar matafiyan tsuntsaye...