Ita zatiyyar so idan ta yi nasarar bayyana haskenta ga masoya ance sukan rikice. Wasu ma sukan makance. Wasu kuma sukan zamo darbar fure da filfilo. Shin idan na zamo darbar fure za ki iya zama filfilon so? Sai dai rayina ba zai so a ce kina sauka a furanni kala-kala ba. Rayina zai so a ce a guna kaɗai za ki tsaya. Kamar dai filfilolin da kan sauya kalolin fukafukansu saboda tasirin furanni da ganyayyakin da ke gudanuwa a rayuwarsu. Ni ma, haka na ke so na zamo gare ki.
Amma kuma, darbar da ke ɗauke da sinadarin so na iya bugarwa ai, ban son ki soma layi a saman iska ki faɗa hannun gizo da ƙoƙi su yi kalaci da ke. Ko kuma ki fara rausayawa ƙarshe ki rikiɗe ki dawo bil'adama ni kuma na ci gaba da zama a ke. Ni zan iya jurar haka na tsawon zamani. Ke fa? Filfilo kan bayyanar da irin ƙaunar da ke a kushewa marar lamba a zuciya. Filfilo kan haske hasken ƙauna a dausayin masoya. Yakan sanya walƙiya ta bayyana a duhun idaniya. Shafukan ƙauna kan buɗu a duk lokacin da fukafukinsa ya kaɗa...
Ko dai mu zama filfilolin ne a tare?
Ni da ke, filfiloli biyu a sararin sama. Mu tanɗo manɗon darbobin ƙauna mu tanɗa wa junanmu. Ƙarshe dai zafin so ya narkar da mu, mu rikiɗe mu zamo darbobin so. Sai mu ci gaba da ƙawatar da duniya da mazaunansa masu tafiya da saƙar zumar ƙauna a rataye a wuya!
Alhassan Maibasira
09/10/25
