Friday, 26 December 2025

Fatana

 

Fatana shi ne a ce, ga ni, ga ki, ni da ke, a cikin madafa muna haɗa shayi. Ki ɗan tsoma ganyen na'a-na’a, ni kuma sai na ɗan watsa kanumfari, ki ɓantari citta ki cilla, ni kuma na ƙyasta mana wuta. Muna zaune muna taɓa taɗi, kina ba ni labarin ƙamshin turaren daren amarci, a haka har ya tafasa, mu juye a tambulan sannan mu dawo mu yi zaune tsakar gidanmu. Ga bishiyu sun mana rumfa, ga sautin ƙoton agwagi ga kukan carar ƴan tsaki, ga magunanmu suna ɗawafi tsakaninmu, sai su wuntsila can sai su mirgina can, kina kallon su kina dariyarki. Ke dai ranki na son mage, ni kuma raina na ƙaunar ki. Rayuwa ce mai sauƙi ni da ke muka shirya, babu tarin burika a cikinta, amma akwai so, akwai ƙauna, akwai aminci, nutsuwa, walwala, nishaɗi, bege, muradi, kewa, ƙulafuci, sannan akwai ni, kuma ke ma akwai ki. 

Wace rayuwa ce za ta kai wannan farin ciki da sururi a zuƙatan masoya? 

Fatana shi ne mu kasance a hakan har abada. Ba tare da mun yi magana ba. Muna kallon ruhikanmu a yayin da ruwan sama ya soma sauka kaɗan-kaɗan, yif, yif, yif. Iska mai cike da ni’ima na ɗan kaɗawa a sannu-a sannu. Mu ci gaba da shan shayinmu. Idan ya ƙare mu shanye na cikin bakunan mu. Ina nufin, ko da yake dai, shi ke nan... To amma kuma mene don kin sumbace ni, mene a ciki don kin sha da ni daga gulbinki ke ma kin tsotsa daga tafkina? Ai so ne ke sa a sumbaci ƙauna. 

Abin nufina, fatana shi ne a ce idan mun ƙare wannan da yamma, a lokacin da rana ta je neman masoyinta, ni da ke, za mu karkaɗa haɗin kofi ɗinmu, mu haɗa ruwan kofi sannan mu haye saman farfajiyar benenmu. Muna masu kallon rana da kyawun launinta, ta ɗan yi ja ta ɗan yi shar, tai fatsi-fatsi, ta yi fes abar ƙayatarwa. 

Fatana, ya kasance ke ɗin ma'abociyar shan shayi ce. Don ni da shayi nake rayuwa. Idan babu shi sai ke to duk ɗaya. Don akwai shayi a saman harshenki. Kanumfari uban ƙamshi  na can haƙarƙarin da ke kusa da gurun wuyarki. Akwai ɗanɗanon ruwan shayi a kowace gaɓarki, kusan duk ganyayyakin shayi a katararki suka turke. Akwai komai a cikinki, wannan laɓɓan da ma harshenki. Zo zauna na ƙwanƙwaɗi shayinki. I, na sani sarai da zafi ai, to ai ke ɗin ce mai zafi. Zazzafar masoyiyata mai tururi! 
Fatana shi ne, idan kika kasance ke ɗin ba ma’abociyar shan shayin ba ce, za ki ba ni dama na shanye ki, bi da bi, gaɓa da gaɓa, a sannu-a sannu. Ina mai lasa, ina kwasar daɗin shayin da ba ya buƙatar kayayyakin shayi. 

Fatana a ce kina karance-karance. Kuma kina iya karance-karance. A ce ga mu nan da safiya, gari ya ɗan fara haske kaɗan, rana ba ta kai ga fitowa ba. A ce ga mu nan a kan kujera, ɗaya a bisan cinyar ɗaya, kina karanta mini daga cikin littafan ruhinki, wai ga ni na sukwano a farin doki, na sha naɗi da amawali, ga alkyabba bisana, hannuna da damin fure. Ke kuma kina tsaye, kin ado kin zayyana, taurari sun fito sun reras suna haskaki, tsuntsaye na rera ƙasidarki, kina dakon jirana na ƙaraso a farin doki na ɗauke ki zuwa birnin.... Ni kada ki ba ni labarin zahiri, sun ciƙa ƙarya da ƙarairayi. So nake ki bani labaran duniyarki waɗanda ba sa taɓa ƙarewa. Ki karanto a yayin da ni kuma na lumshe idanuwana ina mai sauraron wannan muryar taki mafi daɗi fiye da ta sarewa. 

Fatana a ce na san ki zahiri da baɗini, shi ya sa zan so a ce muna kallon junanmu da wata idaniyar can ba wannan ba; wannan idaniyar ta fiye hijabai, ba gani take da kyau ba, wata ran ma fa wai sai na sa tabarau. 

Fatana a kodayaushe, a kullum, safiya da maraice, damina da rani, dare da rana, tsakanin bugun zuciyoyi, tsakanin numfarfashi, tsakanin barci da farke, shi ne: na zama koda moɗar gilashin shan shayinki ne, ko kuma ma shayin ma, yadda zana iya ganin cikinki. Ki haɗiye ni, na shige can cikinki nai zamana abi na. Fatana shi ne a ce na gama saninki. Zahirinki da baɗininki. 

To amma ana ko gama sanin masoyi? 

Alhassan Maibasira
March, 2025

Monday, 22 December 2025

Babu Ranar Da Za Ka Gama Sani(n)!



Matafiyi. Tsaya. Juyo. Saurara. Amsa: Ka sani kuwa? Yaya ake sani ba tare da an sani ba? 
Koma. Zauna. Ladaftu. Karanta. Koda ka sani yanzu ai baka sani(n) ba. 
Nutsa. Haƙa. Keta. Ƙwanƙwaɗa. Koda ka ƙare duka ba za ka sani(n) ba. 
Kwanta. Faraƙa. Kalla! Don duk iya iwon ka, ba za ka kai ƙarshen tekun ba. 

Matafiyi! Tsaya! Rage sauri. Tashi daga tsandauri. Koma can kusa da gulbi. Kalla...!
Yi annashuwa. Ɓace. Rasa kanka a duniya. Nitsa. Taso. Kakkaɓe kurar rigarka. Kalli gizagizai. Yi farin ciki. Sabonta murmushinka. 

Don koda ka sanin ai baka gama sani(n) ba.

Matafiyi! Haraƙo. Biɗa. Kar ka tsaya. Koma dausayi. Zauna kuma. A'a, tashi. Koma tsandauri. Lasa zumar maɗaci. Ɗanɗana maɗacin zuma. Yi shiru! Lula. Kar ka tsaya. Kai can kusa da ƙursiya. Tambaya. Ba amsa? Yi shiru! Tambaya kuma: 

Yaya ake sani ba tare da an sani ba? 

Yi shiru! Saurara: Mene ne sani? Wane ne ya sani? Wa ke tunanin ya sani? Ni ne Masani! Duk wanda yake tunanin ya sani, ai bai sani(n) ba. 

Kai? Kai Wa? 

Ni da nake a kai. Ni ɗin da Na san komai tattare da kai. Ni ɗin da nake Ni, kuma babu wanda yake Ni. Ni ɗin da sani ke zama a Ni. Samaniya ta tsatsafo da yayyafinsa — daga gare Ni. Ni. Ni. To wai shin ma waye Ni?

Kai ne Masani. Ni ɗin ai ban sani ba. Wai shin to: yaya ake sani ba tare da an sani ba? Kar Ka ce baKa sani ba, don na san Ka sani; shi ya sa nake so Ka tsam mini. 

Yi shiru, Matafiyi! Amsar na gun ka tun-tun-tuni. Kuma baka sani ba. Ashe Shi ɗin ne Masani. Kai ɗin ba kowa ne ba. Koma ka karanta. Ci gaba da karatu. Haƙa. Ɗeba. Ƙwanƙwaɗa. Ɓace. Don ko da ka sanin ma ai ba ka gama sani ba. Wai ma, me ake so a sani ne? Soyayya? To me ya kai ka samaniya? Zo bakin gulbi kai ɗaya. A nan za ka tarar da shaya tana ɗiban ruwa a baki don ta tsam wa ƴaƴanta da ke bishiya. “Yaya ta sani ita, tun da ai — kamar— ba ta sani ba?” Ashe amsar na cikinka tun-tun-tuni. Ashe kai ne baka sani ba tun-tuni. Koma ka karanci duniyar Matafiyi, koda ka ma yi hakan, ba za ka gama sani ba!

Alhassan Maibasira
22/07/25

Thursday, 11 December 2025

Kai-komo Tsakanin Duniyoyi Biyu



Jiya na tattauna da taurari. Zance marar tsawo. Cikin ƙiftar idanu. Na kalle su suka kalle ni, sai na zanta da su. Ban san me muka tattauna ba. Amma na san da cewa abu ne muhimmi. Kamar nauyin ganin shudewar rayuka da dama. Da nauyin ganin gilmawar lokaci da ya ratayu a kansu. Da kuma sirrikan da bil'adama suka ɓoye a cikinsu — a duk lokacin da suke kallonsu, a cikin dare mai yalwarsu. Sai dai kuma ban zanta da su ba. Ni na wassafa hakan a raina. Ba su ma san da duniyar nan ba, ba su ma taɓa jin sunanta ba. Shi ya sa ban son zahiriyya - don babu abin da ke fitowa daga ita face uƙuba. Uƙuba mai tsanani, mai bala’in firgitarwa. Gwamma ƙaryar da za ta sanya ni nai rayuwa cikin lumana da gaskiyar da za ta iya hana ni rayuwa gaba ɗaya.

Saboda ina son rayuwar nan. Duk da yake ba ta damu da ni ba. Amma ina son ƴaƴanta. Misali, na yi bakancen gaida bishiyu da tsuntsayen da hayyaci ya riska — da idanuwa ma su ɗauke da kuramen kalmomi. Ina son wannan rayuwa, don ko ba komi ina ganin filfiloli a cikinta. Hakan ya wadatu gare ni. Shi ya sa ban son a ce min bishiya ba ta san da zama na ba. Bishiyar da nake gaisarwa a duk lokacin da na gitta ta ko na gitta kyawawan furanninta da rassanta. A'a fa. Bishiya ta san da zama na. Kuma tana iya amsa gaisuwata. Kalli rassanta na karkaɗawa. Dubi yadda suke rausayawa. Kai, ina son wannan rayuwa!

Rayuwar kuma za ta ci gaba da gudanuwa ba tare da ta kalli tsammatsin da ta jefa ni ciki ba. Za ta ci gaba da tafiya ba tare da waigawa ta kalli kusurwar ƙungurmin dajin da rayi ya maƙale a ciki ba. Ba za ta dawo ba kuma ba za ta sa guguwa ta ciro ni ba. Amma kuma ɗaya daga cikin ƴaƴanta — wato maƙyallu, na ta haskaka mini rayi a cikin dajin. Kuma ina jin, a lokacin da ya ke hakan, babu abin da ya kai hakan matsayi a rayuwata. Ji nake yi tamkar a nan, a daidai wurin, daidai lokacin, rayuwa wata halitta ce da zan iya yin abin da na tsana, na ƙi abin da nake so, domin ta! Duk da yake ina ƙungurmin daji, mai yawan namun daji ma su ban tsoro. Amma tartsatsin hasken maƙyallaye ya baɗe mini ruhi na kasa ganin duhun da ke zagaye da ni. Shi ya sa nake son rayuwa nan. A duk inda kake za ka iya riskar maƙyallun da zai haskaka maka ita...

Jiya ban zanta da taurari ba. Ƙarya nake maku. Na yi tunanin cewa na tattauna ne da su sai na rubuta hakan a wannan takardar. Ita kanta tawadar ta san cewa ƙarya nake yi (wata ƙaryar ma) shi ya sa take ta rangaji tamkar wadda aka wurga a tayil mai tsantsi. Kun ga, matsalar kasancewa ƙasurgumin mai mafarki ke nan; sai ka rasa mene ne zahiri da baɗini. Ba wai kuma don baka san su ba ne. Haka kurum sai su ɓace maka na wani ɗan lokaci daga bisani su dawo. Amma tabbas ina son wannan rayuwa, kuma domin kyawawan ƴaƴanta da ta barbaɗa a ko'ina ne. Wannan ita ce gaskiya. Wata gaskiyar kuma ita ce: na tsani rayuwar nan!

Alhassan Maibasira
11/12/25

Fatana

  Fatana shi ne a ce, ga ni, ga ki, ni da ke, a cikin madafa muna haɗa shayi. Ki ɗan tsoma ganyen na'a-na’a, ni kuma sai na ɗan watsa ka...