Jiya na tattauna da taurari. Zance marar tsawo. Cikin ƙiftar idanu. Na kalle su suka kalle ni, sai na zanta da su. Ban san me muka tattauna ba. Amma na san da cewa abu ne muhimmi. Kamar nauyin ganin shudewar rayuka da dama. Da nauyin ganin gilmawar lokaci da ya ratayu a kansu. Da kuma sirrikan da bil'adama suka ɓoye a cikinsu — a duk lokacin da suke kallonsu, a cikin dare mai yalwarsu. Sai dai kuma ban zanta da su ba. Ni na wassafa hakan a raina. Ba su ma san da duniyar nan ba, ba su ma taɓa jin sunanta ba. Shi ya sa ban son zahiriyya - don babu abin da ke fitowa daga ita face uƙuba. Uƙuba mai tsanani, mai bala’in firgitarwa. Gwamma ƙaryar da za ta sanya ni nai rayuwa cikin lumana da gaskiyar da za ta iya hana ni rayuwa gaba ɗaya.
Saboda ina son rayuwar nan. Duk da yake ba ta damu da ni ba. Amma ina son ƴaƴanta. Misali, na yi bakancen gaida bishiyu da tsuntsayen da hayyaci ya riska — da idanuwa ma su ɗauke da kuramen kalmomi. Ina son wannan rayuwa, don ko ba komi ina ganin filfiloli a cikinta. Hakan ya wadatu gare ni. Shi ya sa ban son a ce min bishiya ba ta san da zama na ba. Bishiyar da nake gaisarwa a duk lokacin da na gitta ta ko na gitta kyawawan furanninta da rassanta. A'a fa. Bishiya ta san da zama na. Kuma tana iya amsa gaisuwata. Kalli rassanta na karkaɗawa. Dubi yadda suke rausayawa. Kai, ina son wannan rayuwa!
Rayuwar kuma za ta ci gaba da gudanuwa ba tare da ta kalli tsammatsin da ta jefa ni ciki ba. Za ta ci gaba da tafiya ba tare da waigawa ta kalli kusurwar ƙungurmin dajin da rayi ya maƙale a ciki ba. Ba za ta dawo ba kuma ba za ta sa guguwa ta ciro ni ba. Amma kuma ɗaya daga cikin ƴaƴanta — wato maƙyallu, na ta haskaka mini rayi a cikin dajin. Kuma ina jin, a lokacin da ya ke hakan, babu abin da ya kai hakan matsayi a rayuwata. Ji nake yi tamkar a nan, a daidai wurin, daidai lokacin, rayuwa wata halitta ce da zan iya yin abin da na tsana, na ƙi abin da nake so, domin ta! Duk da yake ina ƙungurmin daji, mai yawan namun daji ma su ban tsoro. Amma tartsatsin hasken maƙyallaye ya baɗe mini ruhi na kasa ganin duhun da ke zagaye da ni. Shi ya sa nake son rayuwa nan. A duk inda kake za ka iya riskar maƙyallun da zai haskaka maka ita...
Jiya ban zanta da taurari ba. Ƙarya nake maku. Na yi tunanin cewa na tattauna ne da su sai na rubuta hakan a wannan takardar. Ita kanta tawadar ta san cewa ƙarya nake yi (wata ƙaryar ma) shi ya sa take ta rangaji tamkar wadda aka wurga a tayil mai tsantsi. Kun ga, matsalar kasancewa ƙasurgumin mai mafarki ke nan; sai ka rasa mene ne zahiri da baɗini. Ba wai kuma don baka san su ba ne. Haka kurum sai su ɓace maka na wani ɗan lokaci daga bisani su dawo. Amma tabbas ina son wannan rayuwa, kuma domin kyawawan ƴaƴanta da ta barbaɗa a ko'ina ne. Wannan ita ce gaskiya. Wata gaskiyar kuma ita ce: na tsani rayuwar nan!
Alhassan Maibasira
11/12/25

No comments:
Post a Comment