Kamar kullum, Kano ta tashi da zafi—zafin juma’a. Amma maimakon ta ci gaba da taku kamar yadda ta saba, sai ta jirkita daga gwadaben gabaɗaya. Gizagizai suka kumbura lokaci guda, iska ta yunƙuro daga gun da ta je rangadi, da sauri, cikin hanzari, domin ta kawo shelar zuwan wannan baƙo—har yanzu ruwa baƙo ne a Kano, har yanzu ba a saba da saukar shi ba.
Ruwan Kano. Lokaci guda aka soma shi a yau. Kamar dai yadda wannan ruwa yake kasancewa; da yayyafi ake soma shi, cikin daƙiƙu waɗannan ɗigon da ke sassarfa ke sauyawa izuwa masu tsere—masu rige-rigen ƙarasowa ƙasansu. Suna masu gwajin wanda zai riga wani sauka bisan duniya, da mutanenta, da ababen da ke cikinta, ba tare da sun tausaya wa waɗanda ba su samu mafaka ba. Ba tare da sun raga wa gidaje da tubalan da suka yi laushi ba. Ruwan Kano—ruwan sama—ba don tausayin mutanen duniya yake saukowa ba. Saukowa kurum yake.
Ƙarar rufi, kamar kullum, ne ke alamtar da zuwan wannan baƙo gurina. Sai kuma kakkausar bugun da labulaye kan yi wa kusurwar tagar da aka kafa su a kai. Sai kuma ƙura, wasu lokutan. Amma dai, kamar yadda na faɗa a baya, kusan kowane lokaci ƙarar rufi ne ke alamtar da zuwan wannan baƙo.
Tun da aka soma ruwa da yammaci nake waje ina kallon yadda iska da ruwa ke sharafin su babu mai iya hana su: yadda suke ta fyaɗar bishiyar ceɗiya da jerin bishiyun durumin da ke a gabashin fafarandata, tare da karakaina da su—su yi nan, su yi can, ba tare da sun san wajen zuwa ba. Iska na nata, ruwa na nasa.
Amma kuma bishiyun na buƙatar ruwan. Idan babu shi rayuwarsu gimtsewa za ta yi. (Ban san me nake son faɗa ba. Ko kaɗan. Falsafa ce da ban yi niyyar fahimta ba, ko rubutawa ba. Alƙalamina ne ya rubuta. Ko tunanin hakan ban yi ba. Ɗan nema!)
Kamar dai yadda ruwa da iska suka sanya bishiyun nan bulayi, ni ma haka na kasance. Lokaci guda na gan ni a durƙushe a matattakalar da ke kallon ƙawanyayyu, hudaddun tubalan sashen maƙwabciyata. Na ɗauki tsawon lokaci a tsugunne har sai da na tuna da cewar na bar waya a nawa dandamalin benen, haɗe da sanin yayyafin zai iya kai wa wurinta, sannan na tashi.
Farat ɗaya kuma sai ga ni da riga sanye a jikina. Sai kuma ga ni a saman makarin ƙarfen da ke daura da madafana. Sai kuma ganin kaina na yi a ƙasa na buɗe ƙofar gida. Ruwa na ta sauƙa a kaina, amma haka na tsaya a baƙin ƙofa: ƙafa ɗaya a saman dokin-ƙofa, ɗayar kuma a cikin gida; jiki kuwa jingine ga ƙofar.
Iska mai ƙarfi ake ta yi ba ƙaƙƙautawa. Rigata ta yi ta kanannaɗewa ta warware na tsawon lokaci, har ta gaji. Da taimakon ruwan da ke dukan ta ta samu ta manne da fatar jikina. An ta ruwa, kuma ruwan ya ci gaba da fyaɗar jikina. Ko na ce sumbatar jikina. Don ni abin da na ji kenan; a daidai wannan lokaci. Kowane ɗigon da ya sauka a kaina ya baƙonci jikin da ya saba da shi ne, ya zo gaisuwa ga abokin da ya sha haɗuwa da shi ne.
![]() |
Haka dai na tsaya na tsawon lokaci yayin da idanu ke kai-komo tsakanin allunan bakin titi; izuwa motocin da ke ta feshe su da ruwan da ke saman titi; har izuwa masu giftawa a babura, ko a ƙafa, da masu fakewa a shaguna. Zuwa wasu lardukan da na mance da su, waɗanda sai dai na tariyo ƙamshinsu. Ƙamshin ƙasa. Ƙamshin jar ƙasa. Ƙamshin gonar masara a bayan gida. Ƙamshin gida.
Ruwa na ta sumbatar jikina yayin da ni kuma na rungume shi na ƙi sakin sa. Yayin da ya ci gaba da ƙwanƙwasa ƙofofin shuɗaɗen lokaci. Wasu su buɗe, wasu kuma su ci gaba da kasancewa a rufe. A duniyar zahiri kuma, ni ne dai a bakin ƙofa, ina mai rera waƙe da gunjina, waƙen da ban san a ina na san ta ba.
Da rayi ya gaji kuma sai tsintar kaina na yi a farfajiyar gida (ai dama can a farfajiyar nake) ina mai tsalle tsakanin na’ukan intaloki, zubi ɗaya a lokaci ɗaya. Da na gaji kuma sai na dinga dangwalar ruwa ina mai kamanta zane a jikin ƙofa. Na zana alamar murmushi, sai dai ɗigon ruwa ya sanya alamar ta koma ruwa biyu: ga dai murmushin a bayyane, amma a saman fuskar, ɗigon hawaye ne ke ziryowa daga gulbin idanuwa.
Yau na gano cewa na iya zane. Don kuwa na zana ruhina, a yau!
12/06/26

