Shin kun san cikakken sunana? Ba lallai ku sani ba saboda a yadda tsarin ƙasar mu take, suna da laƙabi sun fi tasiri a kan mutum. Ko wanene kuwa. Ko da sarki ne.
Mutane iri na a ƙasar Hausa basu da yawa gaskiya. Ni mai sarauta ne. Ni sarki ne. Kuma na mulki ƙasa mafi girma da faɗi a kasar Hausa. Ni mai sarauta ne kuma ni sarkin ƙasashe har biyu ne.
Ni ne Sarkin Zazzau Muhamman Makau ɗan Isyaku Jatau. Sarki na ƙarshe a mulkin Hausa da yayi mulkin ƙasar Zazzau, a birnin Zaria.
Yanzu na mayar da birni na Abuja. Kun san meye dalili? E to, ci na akai da yaƙi, amma na bazata. Mun je sallar idi a bayan gari domin mu godewa Ubangijin mu a sannan waɗannan Fulanin waɗanda suka ba mahaifina Tuta a baya suka ci garin mu.
Wai shin mene laifina? Na ƙi na kai caffa, da haraji? Wai ko dai saboda na ɗan sirka musulunci da al'adu kaɗan? Ko dan na dawo da wasu abubuwan da mahaifina ya sa aka daina? Ko dai sun dai samu kafar yaka ta ne dan sun ga mahaifina ya bar duniyar tamu?
Ni ma ɗin ban sani ba. Na dai san da mahaifina na raye da baza su yi hakan ba. Shin mene laifina?!
A sanda suka ci garin mu sai mu-yi-mu muka samu damar tserewa; Ni da ƴanuwana da tawagawata da ta saura. Mun tsaya a gundomomi, garuruwa da dama domin su ƙarɓe mu, amma atafau suka ki. Wai suna jin tsoron Fulani. Hahaha! Amma da gaskiyar su, ko nima sun fara bani tsoro. Ji yadda cikin shekaru kaɗan suka cinye ƙasashen hausawa da dama, gashi yau sun zo kaina. To amma, nima baza na raga masu ba, na dai fi son na samu garin da zan zauna ne tukunna kafin mu gwabza dan yanzu a gajiye nake.
Sai da muka nausa can kudancin ƙasar Zazzau a wani gari dake kusa da ƙasar Nupawa (Waɗanda muka taɓa ci da yaki) sannan muka samu masheka. Sai nace wa iyalaina su shiga ciki ni sai naga abinda ya ture wa buzu naɗi yau ɗin nan. Ko ni ko su.
Hakan kuwa aka yi:
Na yaƙe su, na kashe na kashewa sauran kuma suka tsere, wasunsu sukayi hanyar Lafiyan barebari wasu kuma suka koma birnina, Zaria.
A sannan ne na yarda na shiga ƙasar da za'a raɗa wa Abuja nan gaba.
‘Abuja’ dai gari ne mai cike da ƙawa, ga bishiyu ga tsaunika uwa uba ga kuddudufai da dama. Ruwan su kuma ga shi fari ƙal gwanin ban sha'awa ga shi da garɗi da daɗin sha. Shan farko da nayi sai da naji tamkar na bar duniyar!
Ƙabilu ne ke mulkar garin. Na san su. Suna kawo min caffa akai-akai kuma su ke kula da masu tsaron Yankin. Muna basu tsaro su kuma suna biya mana buƙatun mu na sha'anin mulki. Suna da tsantseni kwarai da gaske ga kuma sannin kimarmu. Muna shiga suka bamu kujerar mulkin su, suka yarje mana mu mulke su da ma ƙasar dake zagaye da su. Suka ce ai ba ƙaramar girmamawa bace a ce kun mayar da wannan garin/ƙasar cibiyar mulkin ku, mun gode. Mun gode.
A haka muka fara mulkar garin da za a zo a sa wa Abuja...
x
No comments:
Post a Comment