A lokacin da na farka daga barci, ban tuna da komai ba. Ba abin da na iya tunawa da. Amma fa na san na yi mafarki kuma mafarkin a kan abar sona ne— wacce ban ma sani ba— sai dai kash, na kasa tunawa. Kasancewar ranar larabace kuma ina da aikin yi, sai na share wannan tunanin daga komar zuciyata. Ko-ko nace na yi ƙoƙarin share su. Amma daƙiƙa ba ta wucewa ba tare da na tuna da wannan mafarkin ba. Har ya kasance ga-baki-ɗaya na kasa taɓuka abin kirki a wajen aiki. Ban san menene ya hana zuciyata fizgewa ba a ranar ba, koma menene, zan kasance mai ma sa godiya har abada.
Wannan wuni ne wadda ba zan taɓa mantawa da shi ba. Kafatanin tunanikana suka kasance masu bijire mani. I man! Abin da suka yi min kenan. Kai, har ma raɗa naji suke yi a tsakanin su— ba tare da sun san ina jin su ba— wai ‘idan ya matsa mana sai mu yi masa bore’ ‘Yau ranar Abar son sa ce’, na jiyo wani tunanin nawa na faɗa. Ita ɗaya abar tunanin wacce ta kasance mace a cikinsu dai ta yi shiru tana mai sadda kai ƙasa a yayin da suke wannan maganar. Alamar kunya. Ta hakan ma na san mace ce. Kar ku tambaye ni ta yaya na ke iya ganinsu. Ni ma ban sani ba. Sai dai a duk lokacin da suka fara hirar su na kan ji ni a wani yanayin da ba zan iya misaltawa ba. Sai kuma na fara ganin su. Ga-ba-ki-ɗayan su. ‘Yau kam ranar ta ce, ni ma na yarda ’ na faɗa ba tare da na sani ba. A take sukayi tsit, shirun su ya zafafa har na fara jin sautin sa. Ƙarar sa. Da bugun zuciyar sa. Duk lokacin nan ina wajen aiki. Shi ya sa nace kaɗan ya rage na fizge. Da ko na fizge, da babu mai iya rike ni. Sai dai a gane ni ina gudu ina mai maimaita sunanta— duk da ban sani ba— Abar Mafarki, Abar Mafarki, Abar Mafarki. Abar.... Mafarki...
Sai dai ban fizge ba kuma kamar ita ta riƙo ni a yayin da na nemi na fizge. A tunina. A cikin tunanikana. Ta bayyana mini fuskar ta tare da yi mini magana. Ban amsa mata ba. Saboda tsabar kyawunta, laɓɓana da harasana suka fara tunanin saɓone buɗe su na furta wata kalmar a gaban ta. Kamar ta fahimci hakan, sai tace mani ni ne dai a mafarkin ka. Ni kayi mafarki da. Na san baka san ni ba. I to, nima ban gama sanin kaina ba. “Wane ne zai ce ya san kan sa ma? Babu shi! ”
Ta ce mani ba sai mun san juna ba. Ko a tarayyar sakanni ma za a iya sanin juna — “Ni ma ɗin ai ban musa ba, kawai dai tunano mafarkin ne yake ɗan bani wuya, ga ni nan tsundum cikin ƙunar azaba, amma na cikin zuciya” Kamar ta sani. Kai ta ma sani! Sai ta fara karanta mini mafarkin bi-da-bi, muryarta kaɗai ke tashi a sansanin zuciyata, ko ina yayi tsit, kowa yayi tsit. Bugun zuciyata ko tama ɗauke. Kada wai ta fizge.
Tace mani na so ta sannan na aure ta duk a cikin mafarkin, ita ma ta soni sannan ta aure ni duk a cikin mafarkin. Ta ƙara da cewar ta mutu ne a yayin haihuwa ni ma na take mata baya, duk a cikin mafarkin. Na kasa hakura wai , sai zuciyata ta yarda tayi bindiga. A mafarkin wai babu ahalin mu a kusa da mu. Mu kaɗai ne a wata tsibiri mai nisa. Daga mu sai tsirrai da dabbobin daji. Sai kifayen ruwa. Sai kuma tsagwaron shiru wadda yake cikin kuka da waƙoƙin dabbobin dake dajin.
Tace a kullum idan na tashi daga barci na kan sumbace ta. Ina farawa ne da sumarta; idanuwanta; sai laɓɓanta. Daga nan sai nai zaune ina mai kallonta, a yayin da ita kam ta yi nisa a duniyarta. Tun tana tsorata har ya bi jikinta. Ta cigaba da ce mini wai har sallah ban yi sai nayi hakan. Ta kan tambaye ni dalili sai na ce mata ai Ubangiji nake gaisarwa. Da farko ta ɗauka wasa nake, sai daga baya ta fahimci da gaske nake, sannu har ta gane mai nake nufi. Na murmusa kaɗan.
Tun daga lokacin ta daina tsorata. Sai ma ta daɗa sona. Na ji daɗi ƙwarai. Na lumshe idanuwana ina mai kallon duniyar da wata idaniyar daban— wacce take ruhita a wata ƙogo a ɓoye. Tace bayan sallah sai na cinciɓe ta nai mata wanka. Wai tun da na aure ta ta daina wanka da kanta. Wannan lokacin kam dariya nayi dan na tabbata kaɗan daga aiki na kenan. Sannan sai na dafa mana shafi, muyi zamanmu a waje muna masu kallon tsibirin mu. Ina shan shayi, ita ma tana shan shayi. Ba ma magana idan muna shan shayi. Sai dai, mukan kalli junan mu lokaci-lokaci. Daga bisani ma muka soma kallon ruhikan mu. Tsirara. Muraran. Munyi nisa a sannin junan mu kenan. Soyayyar mu ta kusa matakin ƙarshe! Hakan kam ya burge ni!
Sai tayi shiru, nima na biye mata, kasancewar shiru abu ne wanda nake tsananin so da ƙauna. Shiru na bayyana abubuwan da muka kasa bayyanawa kuma yakan bayyana sirrikan zuciyar masoya. Mun yi nisa a duniyar shirunmu har sauran tunanikan suka fara mita. Suna masu cewa ‘Sai da kika lasa mana Zuma zaki ɓoye ƙwalbar?!’
Ta ɗago ta kalleni a yayin da murmushi ya bayyana a fuskar ta. Murmushinta a kowane lokaci yana canzawa. Yanzu dai murmushi tayi mini irin wanda haƙora ke ɗan haskowa— amma kaɗan. Kamar suna jin kunyar rana ba sa so a gan su. Na daɗe ina kallon murmushin nan, alhali a duniyarmu ita ta ma daɗe da sadda kai ƙasa. Murmushin ƴan daƙiƙu ne kaɗai, amma ni a duniyata, na kai shekara ɗaya ina kallon ta.
Ta cigaba da cewar akwai lokacin da muke zuwa can bakin teku, ni da ita da magen mu marar suna. Ba kuma wani abin kirki muke ba. Kai ba ma abinda muke. Kallon ruwan kawai muke— yadda yake tafiya, rawa, tsalle, da numfashi. Kallon ruwan kaɗai za mu iya yi, domin ita bata iya ruwa ba, nima ban iya ba. Za dai mu iya kallon numfashin ruwan muna ma su numfashi. Ba mu shirya dena numfashi ba tukuna.
Ƙila watarana a lokacin da muka shirya, za mu tafi can bakin tekun, wannan karan shiga za muyi, rike da hannun juna, muna masu kallon ruhikan mu. Tsirara. Muraran. Har abada!
Dec, 2024
No comments:
Post a Comment