Fatana shi ne a ce, ga ni, ga ki, ni da ke, a cikin madafa muna haɗa shayi. Ki ɗan tsoma ganyen na'ana’a, ni kuma sai na ɗan watsa kanumfari, ki ɓantari citta ki cilla, ni kuma na ƙyasta mana wuta. Muna zaune muna taɓa taɗi, kina ba ni labarin ƙamshin turaren daren amarci, a haka har ya tafasa, mu juye a tambulan sannan mu dawo mu yi zaune tsakar gidanmu. Ga bishiyu sun mana rumfa, ga sautin ƙoton agwagi ga kukan carar 'yan tsaki, ga magunanmu suna ɗawafi tsakaninmu, sai su wuntsila can sai su mirgina can, kina kallon su kina dariyarki. Ke dai ranki na son mage, ni kuma raina na ƙaunar ki.
Rayuwa ce mai sauƙi ni da ke muka shirya, babu tarin burika a cikinta, amma akwai so, akwai kauna, akwai aminci, nutsuwa, walwala, nishaɗi, bege, muradi, kewa, ƙulafuci, sannan akwai ni, kuma ke ma akwai ki.
Wace rayuwa ce za ta kai wannan farin ciki da sururi a zuƙatan masoya?
Fatana shi ne mu kasance a hakan har abada. Ba tare da mun yi magana ba. Muna kallon ruhikanmu a yayin da ruwan sama ya soma sauka kaɗan-kaɗan, yif, yif, yif. Iska mai cike da ni’ima na ɗan kaɗawa a sannu a sannu. Mu ci gaba da shan shayin mu. Idan ya ƙare mu shanye na cikin bakunan mu. Ina nufin, ko da yake dai, shi ke nan. To amma kuma mene dan kin sumbace ni, mene a ciki dan ki sha da ni daga gulbinki ke ma kin tsotsa daga tafkina? Ai so ne ke sa a sumbaci ƙauna.
Abin nufina, fatana shi ne a ce idan mun ƙare wannan da yamma, a lokacin da rana ta je neman masoyinta, ni da ke, za mu karkaɗa haɗin kofi ɗinmu, mu haɗa ruwan kofi sannan mu haye saman farfajiyar benenmu. Muna masu kallon rana da kyawun launinta, ta ɗan yi ja ta ɗan yi shar, tai fatsi-fatsi ta yi fes abar ƙayatarwa.
Fatana, ya kasance ke ɗin ma'abociyar shan shayi ce. Dan ni da shayi nake rayuwa. Idan babu shi sai ke to duk ɗaya. Dan akwai shayi a saman harshenki. Kanumfari uban ƙamshi na can haƙarƙarin da ke kusa da gurun wuyanki. Akwai ɗanɗanon ruwan shayi a kowace gaɓarki, kusan duk ganyayakin shayi a katararki suka turke. Akwai komai a cikinki, wannan laɓɓan da ma harshenki. Zo zauna na ƙwanƙwaɗi shayinki. E na san sarai da zafi ai, to ai ke mai zafin ce. Zazzafar masoyiyata mai tururi!
Fatana shi ne, idan kika kasance ke ɗin ba ma’abociyar shan shayin ba ce, za ki ba ni dama na shanye ki, bi da bi, gaɓa da gaɓa, a sannu a sannu. Ina mai lasa, ina kwasar daɗin shayin da ba ya buƙatar kayayyakin shayi.
Fatana a ce kina karance-karance. Kuma kina iya karance- karance . A ce ga mu nan da safiya, gari ya ɗan fara haske kaɗan, rana ba ta kai ga fitowa ba. A ce ga mu nan a kan kujera, ɗaya a bisan cinyar ɗaya, kina karanta mini daga cikin littafan ruhinki, wai ga ni na sukwano a farin doki, na sha naɗi da amawali, ga alkyabba bisana, hannuna da damin fure. Ke kuma kina tsaye, kin ado kin zayyana, taurari sun fito sun reras suna haskaki, tsuntsaye na rera ƙasidarki, kina dakon jirana na ƙaraso a farin doki na ɗauke zuwa birnin.... Ni kada ki ba ni labarin zahiri, sun ciƙa ƙarya da ƙarairayi. So nake ki bani labaran duniyarki waɗanda ba su taɓa ƙarewa. Ki karanto a yayin da ni kuma na lumshe idanuwana ina mai sauraron wannan muryar taki mafi daɗi daga bushin sarewu.
Fatana a ce na san ki zahiri da baɗini, shi ya sa zan so a ce muna kallon junanmu da wata idaniyar can ba wannan ba. Wannan idaniyar ta fiye hijabai, ba gani take da kyau ba, wata ran ma fa wai sai na sa tabarau.
Fatana a kodayaushe, a kullum, safiya da maraice, damina da rani, dare da rana, tsakanin bugun zuciya, tsakanin numfashi, tsakanin bacci da farke, shi ne na zama ko da moɗar gilashin shan shayin ki ne, ko kuma ma shayin ma, yadda zana iya ganin cikinki. Ki haɗeye ni, na shige can cikinki nai zamana abina. Fatana shi ne a ce na gama saninki. Zahirinki da baɗininki.
To amma ana ko gama sanin masoyi?
MA. Maibasira
March, 2025
No comments:
Post a Comment