Da akwai wannan lumanar da bawa kan riska yayin da ya tsinci wannan littafin da ya yi shekaru yana nema a wata ƙurya a cikin ma'adanar taliffai. Duk yadda wannan bawan zai yi kuwa, ba zai iya sa ta a gurbin da ya dace da ita ba.
Ko da zai ce: ya ji wani abu a cikinsa tamkar an kuma haihuwarsa. Ko kuwa: zuciyarsa ta fid da fuka-fuki ta lula samani inda ta zauna tare da rana har ta narke. Ta gwauraye da iska. Ta zama marar nauyi. Ta tsaya cak. Ta yi ta ruri, gunji, tana neman mafari. Ko da zai ce: ya kasance tamkar lokacin da aka halicce sa — kafin a sanya so a cikinsa; kafin ransa ya samu hankali. Wannan lumanar da ya riska tsakanin hankali da rashin hankali.
Ko: ya ji kamar ya mutu baicin yana raye; kamar duniya kowa ya mutu sai shi kaɗai; kamar a samaniyar ma babu giza-gizai; kamar farin cikin mahaifiyarsa lokacin da ya fara kiranta da ‘Mama’; kamar irin walƙiyar da ya bayyana a idaniyarta a san da ya fara ta-ta-ta. Irin tagomashin da ke wanzuwa yayin kallon fuskar masoyiya. Irin yabanyar da ke fitowa daga ƙalbi a yayin kallon murmushin masoyiya. Irin macewar da rai ke yi a lokacin da ya ji ƙamshin turaren masoyiya.
Ko ko ma: ya ji tamkar matalaucin da ya riske alatu a kogo, ko kuwa ma mai karayar arziƙin da arzuƙansa suka dawo. In ya so ya ce: ya ji kamar yaron da ya soma ɗanɗanar romon ilimi: garɗin sa, zaƙin sa, mai yawan sukari. Annashuwar da ke ɗarsuwa a rai idan ya amsa tambaya daidai; Iskar da ke wantagaliliya da kafatanin tunaninsa a yayin da ake tafa mai; rijiyar shauƙin da ke ta amayar da wuta a maimaikon ruwa; yanayin da ya tsinci kansa a lokacin da rayuwa ta lasa masa zauƙin da ke a miyar ilimai.
Duk waɗannan ba za su bayyana iya girman yanayin da ya shiga ba. Duk waɗannan ba za su haska wa makaranci iya tumbatsar da ɗan ƙaramin dunkulen da ke a ƙirjin bawan nan ke yi ba. Duk waɗannan sai dai su kwatanta wa mai karatu iya budum-budumar da bawan nan ya yi a cikin kogin farin ciki.
Kuma ya tsinci kansa a wannan yanayin ne a wata ƙurya, wadda haske bai wadata ta ba, wadda ƙura ce ke ƙawata ta, wadda aka daɗe ba a leƙa ta ba. A can wani ɗan ƙaramin ɗaki mai ɗauke da tulin litattafai.
08/07/25
No comments:
Post a Comment