Akwai wasu halittu da ke nasarar killace rai a matsayin ruwa su sa shi a salkarsu. Su ba sha za su yi ba, ba kuma fito da ran za su yi ba har sai sun kai madakatarsu. Sai su zubar da ruwan walau a ƙasa ko a cikin randar gidansu. Idan ya ci sa'a suka saka shi a randar, to ba ƙaramin farin ciki zai yi ba, saboda ko ba komai: zai sirku da ruwan gidansu, za su tsotsa daga sinadaransa, zai kuma dinga jin sautin muryarsu, da ma ƙamshin turaren su. Zai kuma shige can cikinsu. Zai iya tagomashi da sirrikan da ke kwance a cikinsu.
Idan kuma watsar da ruwan suka yi a ƙasa, sai ya yi ta ratsa yashi da tsakwankwani; tsutsosi da ƙananun halittu; aljanu har ma da ɓurɓusan ƙasussan bil'adama da dabobbi; ƙasashen zamanin da da ƙasa ya rufe; kududdufai da ma’adanar kayayyakin alatu; har ya isa inda zai haɗu da sauran rayuka kamar sa, inda suke zaune a daira, ƙafafun kowannensu a tankwashe. Suna masu karatu daga wani littafi — mai kama da littafin so.
Abin mamaki kuwa, duk cikinsu, babu wanda ya san sunan halittar da ya haɗu da. Babu wanda ya damu ya san sunanta. Kawai makillaciyar ransu ce suke so, ita ɗin da ba ta da suna.
Su kuma waɗannan halittun ba su ma san da sun yi hakan ba. Ƙila murmushi suka yi kawai, ba su san da cewa a take rai ya narke ba; saboda zafin wannan murmushin a gare sa. Saboda tsananin farin cikin tozali da wushiryar makillaciyar ransa.
Ƙila kuma kallon sa suka yi da waɗannan idaniyar ta su, wandararru, masu kama da rana a tsakiyar sahara, sai ransa ya fara amon wutar ƙaunar wannan idaniya; ya kasance mai fata ya zama ko da ruwan idaniyar ne — sai kuma ya zama! Amma maimakon ya ƙare a idanunta sai ya gan shi a salkarta. Amma kuma ita ke riƙe da shi a hannunta. Hakan ya wadatu a gare sa!
Ƙila kuma kiran sunansa ta yi, sai kawai ya ga ransa ya fara fiddo da fuka-fukai. Ransa ya zama kamar wani mala'ika. Ya yi ta harbawa sama har ya cimma zara ya zauna a bisanta. Sai ya narke. Sai ya zamo ruwa. Ya sulalo daga sama ya shige cikin salkarta.
Akwai wasu halittun da ke ƙona rai, su narkar da rai, su zuzuta rai, su haukatar da rai, su kuma makantar da rai. Yadda suke so — duk da yake ba lallai da sonsu ba, amma shi rai bai damu da wannan ba.
Akwai waɗannan halittun a ko'ina. Kuma a koyaushe idan na haɗu da su, sai na zame ɗaya daga cikin nau'kan ruwan salkarsu.
17/06/25
No comments:
Post a Comment