Suka tambaye ni wani guziri na tanada idan na kai ga madakatata, sai kawai na murmusa.
Akwai shatin sumbatata akan kowane fure a duniya. Akwai taswirar rayina a kowacce kusurwar duniyar taurari. Gajimare ne shigifar ruhina. Da rana ta ƙona ni ban koka ba, da mamakon zubar ruwa ya gume ni ban yi faɗa ba, da ambaliyar ta wuce wuya ban nuna ba. Kuma ba su hana ni ci gaba da tafiya ba. Saboda ni matafiyi ne. Na dai huta a dausayi na ɗan lokaci sannan na ƙara gaba.
Ina da lambunan da na ƙera don tsuntsaye kurum. Ina kuma da akurkai bila’adadin da ƙofofinsu suka kasance a buɗe a zuciya. Na raya bishiyu da ƙauna. Na ciyar da tsirrai da sona. Akwai tambarin fatan alheri a bisan fuskata, na buga tambarin a dukkanin halittar da na riska.
Ina da son da ya zam sinadarin fasa duwatsu. Ina da ƙaunar da ta nausa gun su Gijimasu. Na watsa irin farin ciki a gonaki marasa adadi. Na ba da aron salkata ga abokai matafiya.
Samaniya ta yi wa zuciya ado. Rana ta harraƙa ruhi da ɓargon zuciya. A iya tafiyar da na yi— na ɗan lokaci ƙalilan— ban cika duniya da kalamai ko surutai ba, amma zantuttukan da ya wanzu tsakaninmu sun fi na kowa a duniya.
Idan na kai ga madakatata, ba ni da wani guziri da zan ba da. Zan dai ce a tambayi turɓaya da ganuwai; ƙoramu da ƙwaɗi; tsuntsaye da bishiyu, da duk wata halittar da na baro a duniya — sun fi ni sanin da wani guziri na taho. Sun fi ni sani!
Alhassan Maibasira
24/04/26

No comments:
Post a Comment