Sunday, 19 April 2026

Kuma Ina Da Ke

Ina da gajimare, mai yabanyar da ruwan lumana a turɓayata. Ina da hasken rana, mai ciyar da ruhi da kumalonsa da sanyin safiya. Ina da tsuntsaye, masu tuna mini da dausayin jannatun da nakan sadu da masoyiya. Ina da shirun darare, mai lulluɓi jiki da ruhi da bargon annashuwa da ƙulaficin shekarun baya; mai turare jiki da ƙamshin miskin da ya wanzu a dausayu shekarun baya; mai lallafta wa zuci naɗin riguna masu nauyi da ƙwazzaba zuci; mai turo da hasken taurara, daga can sama, ya ratsa ta sarari da labule, ya ziyarci idanu; mai haska majigi a jikin bangon da ke bayyana shaukuna (kaɗai) na rayuwar baya da hayyaci ya manta da su.

Ina da sassanyar iskar da ke zuwa ga taliƙai don busa musu sarewa, don kaɗa musu ganga, don buga musu tambari, don tuna musu ita ce uwargijiyar waccan zamani, don busa musu sirrikan da ya rayu tsawon zamani. Ina da rumfar samaniya mai taswirai da alatai, mai dausayu da kushewu, mai kwaranyar da ruwan zuma-maɗaci. Tamkar Rumfa ga masoyi da magauci.

Sannan ina da ke, ke wadda ta wanzar da ni
Sannan ina da ke, wadda ta samar da ni
Sannan ina da ke wadda ta lulluɓe ni
Sannan ina da ke, Ƙoramar janna gare ni
Kuma ina da ke, taurarar haskaka ni 
Kuma ina da ke, zuma-maɗaci a tunani
Kuma ina da ke, rumbun sirrika na ni 
Kuma ina da ke, Ƙauniya da ta ɓoye a ruhi
Kuma ina da ke, iska wanzuwar dauri
Kuma ina da ke, a ruhi da tunani
Kuma ina da ke, A harrufa a duk layi
Kuma ina da ke , A shiru mai gurnani
Kuma ina da ke, Ke; taurarar samani

13/04/26

No comments:

Post a Comment

Kuma Ina Da Ke

Ina da gajimare, mai yabanyar da ruwan lumana a turɓayata. Ina da hasken rana, mai ciyar da ruhi da kumalonsa da sanyin safiya. Ina da tsunt...