Sunday, 27 April 2025

Wani abu mai kama da tattaunawa tare da wani ‘Matashi’

Wannan tattaunawa ce da ba ta da mafari, kamar yadda tattaunawar yau da kullum take. Ba wai ba ta da mafari ba ne a haƙiƙanin ta, kawai dai. Kawai dai...

Bayan na tsakuro daga cikin wani rubutu na, wannan ‘matashi(n)’ wanda nake ji kamar ni ne, sai dai, ba ni ɗin bane, cikin tasa hikimar, ya suɗaɗo da tasa mahangar har ya zamana mun ta hangawa junanmu abubuwan da bamu san da akwai su a ruhi kanmu ba. Sunan wannan Matashin Mujahid Yusuf (Matashi). Ga yadda wannan abu mai kama da tattaunawa ya kaya:

Mujahid: 

“Wannan rayuwa haka sai ka ce ba a duniya ba!

Ko da yake da ma, wani shiryayyen mafarki ne da yake abin yiwuwa kaɗai a alam ɗin mafarki. Wannan wani bankaɗar sirrin zuciya ne, wani tonon sililin binne-binnen da zuciya ta rufe na muradi ne.

Abin birgewa, abun kuma tambaya, shin mutane yanzu na samin alaƙantuwa da ababan da ke kewaye da su? Misalin sautin tsallen tsomuwar ganye cikin kofin shayi?”

Ni:

Komai mai yiwuwa ne a duniyar mafarkai. Ba abin da mutum ba zai iya wassafta wa ba. Ba abin da mutum ba zai iya tunanowa ba. Babu kogin mafarkan da mutum ba zai iya afkawa ba. Babu gajimaren da, in ya so, ba zai iya keta wa ba. 

Duniyar mafarki kenan, babu wani abin da ka iya kawo masa cikas. Babu Ubangiji, sai wanda ka ƙera wa kanka. Babu addini, sai wanda ka tufata kanka da shi. Duk da yake Ubangijin ne ya halicce ta, sai ya zama Bai sanya ma ta bango ba. Ma'ana dai, bata da iyaka. Amma ka ga tamu duniyar da iyaka ai. Akwai abubuwan da za mu iya yi, akwai kuma waɗanda ba za mu iya ba, akwai waɗanda sai mun yi da gaske sannan mu iya ma. 

Ashe ma iya cewa kenan, duk wata iriyar soyayya ko ma wani yanayin da kaso, duk za ka riske su a duniyar mafarki, saboda ba ta da iyaka.

Babu abin da mutum ba zai iya alaƙantuwa da shi/ita ba. Har ma akwai abubban da wasu suka ma fi alaƙantuwa da shi fiye da komai. Wasu za kaga motsin bishiyu ne. Wasu kuma motsin busassun ganyayyakin da ke ƙarƙashin bishiyun ne.

Akwai bambanci tsakanin abin da mutum ya wassafta da abin da ya rubuta. Duk inda marubuci ya kai wajen sarrafa zuciyarsa da iya rubutu. Akwai wani tasgaro da rubutun yake samu. Ma'ana dai, ba za mu taɓa iya yin daidai abin da ke kogin zuciyoyin mu ba. Sai dai mu kwatanta. 😊”

Mujahid: 

“Haka. Rubutun namu ne ke da iyaka, ko kuwa mu ke da iyaka a rubutun?”

Ni: 

To fa! Ina jin duka biyu ne. Idan muka tsaya muka ɗan duba shi karan-kan-sa tsarin rubutun. 

Da farko dai, sai mutum ya yi tunani sannan ya rubuta. Tsakanin tunanin da rubutun akwai kalmomin da ka iya suɓucewa. Akwai sakin layin da ka iya maƙalewa a wani saƙon ƙwalwar mu. 

To kuma idan ma muka fara rubutun, mu kan mu, muna sane da wasu wuraren da baza mu so mu taɓa ba, ƙila saboda tasirin Al'adu, Addini, ko ma tsarin ɗan Adam na sa. 

Saboda haka, ko da rubutun ya zo saman alkalamin mu, mu kan daƙushe alƙalamin ruhin mu da kaɗan, domin dai mu samu damar rubutun ba tare da waɗannan abubuwan da ba ma ra'ayi ba.”

Mujahid: 

“Kalmominka sun nuna, ko da ba haka ka nufa ba, cewa mu ke da iyaka a rubutun bisa ababan da ka jero na al'adu, addini da sauransu.

A mahanga ta adabi wannan kam naƙasu ne ga rubutu domin shi adabi ba shi da ɗayan abubuwan da ka lissafo. Sukan ce, kamar mazubin kwalba ne.

A ma'aunin mu'amalantar ɗan adam kuwa, wannan daidai ne. Kuma shi ya fi daidai da fahimtar Addinin Islama. Shi ya sa Yusufun Nabahani yake cewa, ‘Ai ba duk abin da aka sani ne ake faɗa ba.’ Wannan a babin ilimi ma ke nan da yake abin dogaro, balle kuma a babin ƙirƙira.”

Ni: 

“A ƙarshe dole hankali ya yi tasiri ga rubutu; ko muna so, ko ba ma so.”

Godiya mai tarin yawa ga Mallaminmu Mujahid! 


27/04/25

Friday, 25 April 2025

Kukan Kurciya

Akwai wata kurciya da ke zuwa bakin tagata kullum da safiya. Kukanta mai daɗi ke tayar dani daga barci. Na kan kwashi lokaci mai tsayi ina kallonta, ina sauraran kukanta, ina mai ninkaya cikin duniyar mafarkaina wasu lokutan, har da mafarkanta— idan naci sa'a. A cikin duniyar tata mafarkai ne a jere da burika irin tasu ta dabbobi, kar ka tambaye ni wai ashe suna da mafarkai. Ca akai kai kaɗai ne mai iya yin su? 

Ƴar alkawari. Da hakan nake kiranta. Baiwar Allāh abar kwatance. A duniyar tata akwai ma'adanar rayuwarta ta baya. Nan na leƙa wata rana. Sai na ganni a wani kufayi; kango mai haske abin haskakawa. Na gano iyayen ta da ma ƴanuwanta su su duka a zaune. Bayani ne kan yadda rayuwarsu ta ke kasancewa a wannan duniyar. Mahaifin ne ke magana yanzu; baƙi, ƙaƙkaura, idanunsa ja tamkar na Hasbiya. Ya na riƙe da ƴar sanda, alamar tsufa. 

“Iyayen mu sun shaida mana cewa; an shaida wa iyayen su cewa; kakanninsu sun taɓa riskar wani zamani mai ƙayatarwa. A lokacin babu injina ballantana motoci. Saboda haka akwai bishiyoyi da dama, inda ahalinmu ke rayuwa. Rayuwa ce mai sauki a lokacin; babu ƙara, babu datti, babu shara, babu kiɗa; sannan kuma akwai gida. A kowane lokaci suna iya komawa gida ba tare da sun shiga cikin taskar wasi-wasin kasancewar yana nan ko akasinsa ba. Lokacin fa ba a cire masu bishiyu ba bisa ka'ida ba. Kamar na taɓa jiyo kakana Alto yana cewa lokacin Hausawa ke mulkin ƙasar Hausa ba Fulani ba. Sai dai ban san takamaiman lokacin wani sarki ne ba. Ku faɗa mini yarana: shin rayuwa bata fi sauki a da ba. Yanzu ko da ba a cire bishiyoyin ba, ruwan saman mai ƙarfi da ake yi zai cire shi. Duk saboda halayyar bil'adaman dake zamanin mu.”.                                   

Sai mahaifiyar tai caraf ta ƙara da cewar: 

“Ai ko jiya sai da leda ta sarkafe ƙafafuwan Lami da taje farautar ƙwari. Da ƙyar na samu na iya cirewa. Kalli har yanzu da sauranta a cikin yatsunta. Har sai lokacin da Allah ya yi. Abin da ba su ma ganewa— wato su bil'adaman nan— shi ne: abubuwan nan sun ma fi cutar su. Jiya nake ji, a tagar Mallam Sani, wai ga-baki-ɗaya makwararar Jakara ta toshe, saboda haka, mazauna kusa da ita su kiyaye, kasancewar idan aka yi ruwa mai ƙarfi, za a iya ambaliya. Ko-ko ma zafin nan da ake ta zabgawa, ko mu nan da-ba-dan tsarin hallitar da Ubangiji Ya yi mana ba, ai da wani zancen ake. Kuma duk me yasa hakan? Rashin shuka bishiyoyin da za su ci karo, koma su daɗa, waɗanda ake cirewa, da wasu dalilan can.”

Babban ɗan, wanda ya kasance ma'abocin karance-karancen tarihi, sanye da ɗan madubinsa ya ƙara da cewa: “Kun ga kuwa rayuwa ta fi daɗi a lokacin baya. Ina-ma- ina-ma, zan iya komawa can. Na biye wa tawagar Sarkin Zazzau Muhamman Makau lokacin da aka ci ƙasar sa da yaƙi. Yana tafiya da tawagarsa ina biye masa, har su isa Abu-Ja. Nayi zamana a can. Ina ma a ce a wancan ƙarnin a ka haifemu! Ga bishiyu, ga tsaunika, ga ƙoramai, ga ruwa mai kyau. Rayuwa mai daɗi! Uwa uba, ga tsafta. Gari ƙal-ƙal sai kace Aljanna.”

Shin ya Aljanna take? Ka taɓa zuwa ne?” In ji kurciyata, wacce ta kasance a kishingiɗe a saman tsabar da ke kwance a kangon, kanta na kan fika-fikin mahaifiyarta. Sai na ga duka manyan sun ƙalƙale da dariya. Mahaifiyar ko ta janyo ta, ta lakaci hancinta da nata hancin cikin zallar so. 

Mahaifin ya yi gyarar murya ya na mai cewa: “lokaci ya yi, yanzu ina muka dosa?”. A daidai lokacin sai na jiyo ƙarar injin ‘rum-rum-rum’. Sai muka jiyo ‘dum!’ Mai ƙarfi. Na waiga, kafin na juyo kuma, sai na jiyo “Fap...fap...fap”...

Mahaifiya ke jan gora, mahaifin ke bayan ayarin, Ƴaƴayan na tsakiya. Tafiya suke kamar ba za su tafi ba . Da suka nisa sai duk suka juyo, suna masu kallon gidansu a ƙaro na ƙarshe. “Rrrr”— ƙara ya tsaya cak. Amma bishiyarsu— gidansu— babu. Sun tafi kenan. Har abadan... a-ba-da.

Da na dawo zahiriyya, sai na nitsa a cikin kogon tunani. Abubuwan da suka wakana tamkar a mafarki. Na yi mamaki ƙwarai da ba su lura dani ba. Wai shin ko na mutu ne?... Amma kuma wani abu guda daya kasance yana ta yi min kulumboto a cikin zuciyata; kamar na san wurin ko ma na taɓa rayuwa a inda na riske su. Kamar na san kangon nan. Kamar na san ginin nan. Kai, na ma san su! Da na nitsa sai na fahimci cewar, ai inda ma suke tsaye a nan ɗakina yake. Inda aka yi wa ƴaƴayan huɗuba ai a cikin gidan nan yake. Bishiyar da ma na tsakiyar kangon ne. 

Dabbobi ma, kamar ɗan Adam ba sa mance gida. Dabbar ma tsuntuwa. Tsuntsuwar ma Kurciya. Ashe, shi ya sa, a kullum take tashina daga barci. Kukan da take yi ai tuni take min, magana take min, wa'azi take yi min: “Duk inda halittar Ubangiji zai kai ya kawo ba za ya taɓa mantawa da gida ba. Nan ne gidanmu, ba zan iya mantawa da shi ba.”

Washegari na tashi a makare kasancewar ba ta zo ba. Mai tashina ba ta. Sati yazo ya wuce, wata ya rarrafa a sukwane, shekara ta zo a guje. Lokaci mai tsayi ya ja. Amma kullum da tunanin kurciyata nake tashi daga barci.

 “Baba, lokacin shan shayi yayi” na jiyo ɗan autana Sambo na faɗi. Na tashi, na shirya, na ishe su a ƙarƙashin bishiyar da na dasa shekarun baya— irin wacce na gani ne a mafarkin kurciyata. Kuma a inda na ganta a nan na kuma dasa ta. Ga kujeru, ga shayi, ga iyali, sannan ga Kurtattakina a saman bishiya, suna ta kukan su. “Kukan Kurciya dama ai jawabi ne.” ko ni ne na faɗa, ko Kurtattakin dake saman bishiyar ne, ba na ce ba.

MA. Maibasira

24/04/25





Wednesday, 2 April 2025

Matata Ko Uwargijiya?

Ƴa ta Saude ta tambayeni wai shin me yasa nake kiran Matata da Uwargijiya. A lokacin muna gaɓar bakin kududdufin mu na bayan gida ne. Tace mahaifin su Ilhambba haka yake kiran matarsa ba. Sai nayi mata murmushi na jawo kofin shayina ina sha. Na cigaba da murmushi...

Taya zan buɗe wannan labarin? Ko nima ban sani ba. Ni na kasance ma'aikacin gwamnati ne wadda yake da hazaka wajen ganin ya gabatar da aikin sa da tsoron Ubangijin sa. Ta haka na haɗu da Matata, farin ciki na. A take damuwata duk suka kau, lokaci guda naji idan har ban mallaketa ba to zan iya ƙona komai!

Na hadu da Matata ne a wajen cin abinci tayi odar filter kofi, wani kofi ne wadda da ƙauna ake sarrafa shi, wato idan har babu kaunar to bai cika ba. Ni kuma ina shan shayi a can baya. A ranar na hadu da ita na biyu saboda mun taba haduwa tabbas kafin a aikomu nan duniyar. 

Tazo ta zauna a teburin da ke kallo na tana mai kallon tsuntsaye da ke ta kullumboto a gajimare. Rana ta kusa komawa gida inda za take haskawa mijin nata hasken ta. Itama Uwargijiya ce!

Bamu ce wa juna komai ba duk da zuciya ta taso tayi amma sai bakina yaki amincewa. Itama a nata bangaren haka akayi. Sai muka koma zantukan da zuciyoyinmu kaɗai ba tare da magana ba. Ina nufin sai muka kasance masu magana da shirun mu. Ban san dai mai zuciyoyin na mu suka tattauna ba amma tabbas na san sun yi magana. Shiyasa ban mamaki ba da na kuma ganinta washegari a wata dandalin da ake shaye-shayen shayi. Dama ai Ruhikan ma'abota shan shayi a koda yaushe a hade suke. Da sunga juna sai su fara hajijiya. 

A ranar dai mun yi magana. Na ce mata sannu ta ce yawwa. Amma a doron wadannan kalmomin guda biyu mun kamalla duk zantukan da ya kamata muyi— na gama saninta itama haka. Washegari kam sai gidansu. Mukai aure cikin dan kankanin lokaci. Muka zama ma'aurata.

A gurin aiki kam mun samu wata kafar samun kuɗaɗe kuma na ƙi na fada mata gaskiya. An dau lokaci a haka har muka samu Saude. Wacce ta kasance cikon farin ciki na. Na kasance a can sama tare da gajimare saboda tsananin farin ciki. 

A ranar da Matata ta gane harkar da nake yi a ofis, ranar ce mafi duhu a rayuwata domin a lokaci guda na hango mutuwata -idan babu ita. Tace Mani dama abin da kake yi kenan? Tace Mani baka tsoron Allah ne? “Ba haka kake ba shin mune muka saka? To zamu bar maka gidan. ”

Nayi shekaru ina son na bar wannan harkalar, Nayi shekaru ina son na gujewa wannan ɓarnar da nake yi amma na kasa. Na roki Ubangijina ya sa na daina amma na kasa dainawa. Amma da wadannan kalmomin suka fito daga bakinta sai naji komai ya gushe. Ruhina ya zama kamar fanko, babu komai cikinsa sai tsagwaron shiru. A haka nai ta luluwa har na riski abubuwan da ba zana iya bayyanawa anan ba. Ni da Ruhina muka amsa, mukayi ta maimaitawa. “Ke uwargija ce!”

I Matata Uwargijiya ce kuma hakan nake kiranta. Uwargijiya. Amma Saude ba za ta fahimta ba. Hakana masu bi na. Shin ta cancanci hakan. Ni dai na san ta ma so ta fi hakan!


2024

Sidi-Gibran bin Pessoa

The inscrutable pain of existence. The nonchalant stings of bees of life. That pain, that sweet pain... 

to want, to like, to love, to exist, to do all things following the rules of man. To leave, to breathe, to eat, and then sleep. To exist in the most pathetic way one could ever think. To sleep without a dream. Just blank without anything, just you and your emptiness

To kill the ability to think. To not think. To not feel, to just be; like an endless piece in the infinite space. To be nothing. To want nothing. To love nothing just you and your senseless self

To live life in transit, constantly moving. To live life in a constant circle. Trapped there for eternity.To not know what to think and want to not know how to think. To be! 

To not search. To not learn. To just be! 

To only exist in dreams 

to live dreams in awakening 

to only talk in dreams 

to live dreams in awakening 

To know nothing, learn nothing, discover nothing —

To be a vast land composed of Nothing, something, everything. To be an empty, empty land


7th November 2023

Abar Mafarki

A lokacin da na farka daga barci, ban tuna da komai ba. Ba abin da na iya tunawa da. Amma fa na san na yi mafarki kuma mafarkin a kan abar sona ne— wacce ban ma sani ba— sai dai kash, na kasa tunawa. Kasancewar ranar larabace kuma ina da aikin yi, sai na share wannan tunanin daga komar zuciyata. Ko-ko nace na yi ƙoƙarin share su. Amma daƙiƙa ba ta wucewa ba tare da na tuna da wannan mafarkin ba. Har ya kasance ga-baki-ɗaya na kasa taɓuka abin kirki a wajen aiki. Ban san menene ya hana zuciyata fizgewa ba a ranar ba, koma menene, zan kasance mai ma sa godiya har abada.

Wannan wuni ne wadda ba zan taɓa mantawa da shi ba. Kafatanin tunanikana suka kasance masu bijire mani. I man! Abin da suka yi min kenan. Kai, har ma raɗa naji suke yi a tsakanin su— ba tare da sun san ina jin su ba— wai ‘idan ya matsa mana sai mu yi masa bore’ ‘Yau ranar Abar son sa ce’, na jiyo wani tunanin nawa na faɗa. Ita ɗaya abar tunanin wacce ta kasance mace a cikinsu dai ta yi shiru tana mai sadda kai ƙasa a yayin da suke wannan maganar. Alamar kunya. Ta hakan ma na san mace ce. Kar ku tambaye ni ta yaya na ke iya ganinsu. Ni ma ban sani ba. Sai dai a duk lokacin da suka fara hirar su na kan ji ni a wani yanayin da ba zan iya misaltawa ba. Sai kuma na fara ganin su. Ga-ba-ki-ɗayan su. ‘Yau kam ranar ta ce, ni ma na yarda ’ na faɗa ba tare da na sani ba. A take sukayi tsit, shirun su ya zafafa har na fara jin sautin sa. Ƙarar sa. Da bugun zuciyar sa. Duk lokacin nan ina wajen aiki. Shi ya sa nace kaɗan ya rage na fizge. Da ko na fizge, da babu mai iya rike ni. Sai dai a gane ni ina gudu ina mai maimaita sunanta— duk da ban sani ba— Abar Mafarki, Abar Mafarki, Abar Mafarki. Abar.... Mafarki...

Sai dai ban fizge ba kuma kamar ita ta riƙo ni a yayin da na nemi na fizge. A tunina. A cikin tunanikana. Ta bayyana mini fuskar ta tare da yi mini magana. Ban amsa mata ba. Saboda tsabar kyawunta, laɓɓana da harasana suka fara tunanin saɓone buɗe su na furta wata kalmar a gaban ta. Kamar ta fahimci hakan, sai tace mani ni ne dai a mafarkin ka. Ni kayi mafarki da. Na san baka san ni ba. I to, nima ban gama sanin kaina ba. “Wane ne zai ce ya san kan sa ma? Babu shi! ”

Ta ce mani ba sai mun san juna ba. Ko a tarayyar sakanni ma za a iya sanin juna — “Ni ma ɗin ai ban musa ba, kawai dai tunano mafarkin ne yake ɗan bani wuya, ga ni nan tsundum cikin ƙunar azaba, amma na cikin zuciya” Kamar ta sani. Kai ta ma sani! Sai ta fara karanta mini mafarkin bi-da-bi, muryarta kaɗai ke tashi a sansanin zuciyata, ko ina yayi tsit, kowa yayi tsit. Bugun zuciyata ko tama ɗauke. Kada wai ta fizge. 

Tace mani na so ta sannan na aure ta duk a cikin mafarkin, ita ma ta soni sannan ta aure ni duk a cikin mafarkin. Ta ƙara da cewar ta mutu ne a yayin haihuwa ni ma na take mata baya, duk a cikin mafarkin. Na kasa hakura wai , sai zuciyata ta yarda tayi bindiga. A mafarkin wai babu ahalin mu a kusa da mu. Mu kaɗai ne a wata tsibiri mai nisa. Daga mu sai tsirrai da dabbobin daji. Sai kifayen ruwa. Sai kuma tsagwaron shiru wadda yake cikin kuka da waƙoƙin dabbobin dake dajin. 

Tace a kullum idan na tashi daga barci na kan sumbace ta. Ina farawa ne da sumarta; idanuwanta; sai laɓɓanta. Daga nan sai nai zaune ina mai kallonta, a yayin da ita kam ta yi nisa a duniyarta. Tun tana tsorata har ya bi jikinta. Ta cigaba da ce mini wai har sallah ban yi sai nayi hakan. Ta kan tambaye ni dalili sai na ce mata ai Ubangiji nake gaisarwa. Da farko ta ɗauka wasa nake, sai daga baya ta fahimci da gaske nake, sannu har ta gane mai nake nufi. Na murmusa kaɗan.

Tun daga lokacin ta daina tsorata. Sai ma ta daɗa sona. Na ji daɗi ƙwarai. Na lumshe idanuwana ina mai kallon duniyar da wata idaniyar daban— wacce take ruhita a wata ƙogo a ɓoye. Tace bayan sallah sai na cinciɓe ta nai mata wanka. Wai tun da na aure ta ta daina wanka da kanta. Wannan lokacin kam dariya nayi dan na tabbata kaɗan daga aiki na kenan. Sannan sai na dafa mana shafi, muyi zamanmu a waje muna masu kallon tsibirin mu. Ina shan shayi, ita ma tana shan shayi. Ba ma magana idan muna shan shayi. Sai dai, mukan kalli junan mu lokaci-lokaci. Daga bisani ma muka soma kallon ruhikan mu. Tsirara. Muraran. Munyi nisa a sannin junan mu kenan. Soyayyar mu ta kusa matakin ƙarshe! Hakan kam ya burge ni! 

Sai tayi shiru, nima na biye mata, kasancewar shiru abu ne wanda nake tsananin so da ƙauna. Shiru na bayyana abubuwan da muka kasa bayyanawa kuma yakan bayyana sirrikan zuciyar masoya. Mun yi nisa a duniyar shirunmu har sauran tunanikan suka fara mita. Suna masu cewa ‘Sai da kika lasa mana Zuma zaki ɓoye ƙwalbar?!’

Ta ɗago ta kalleni a yayin da murmushi ya bayyana a fuskar ta. Murmushinta a kowane lokaci yana canzawa. Yanzu dai murmushi tayi mini irin wanda haƙora ke ɗan haskowa— amma kaɗan. Kamar suna jin kunyar rana ba sa so a gan su. Na daɗe ina kallon murmushin nan, alhali a duniyarmu ita ta ma daɗe da sadda kai ƙasa. Murmushin ƴan daƙiƙu ne kaɗai, amma ni a duniyata, na kai shekara ɗaya ina kallon ta. 

Ta cigaba da cewar akwai lokacin da muke zuwa can bakin teku, ni da ita da magen mu marar suna. Ba kuma wani abin kirki muke ba. Kai ba ma abinda muke. Kallon ruwan kawai muke— yadda yake tafiya, rawa, tsalle, da numfashi. Kallon ruwan kaɗai za mu iya yi, domin ita bata iya ruwa ba, nima ban iya ba. Za dai mu iya kallon numfashin ruwan muna ma su numfashi. Ba mu shirya dena numfashi ba tukuna. 

Ƙila watarana a lokacin da muka shirya, za mu tafi can bakin tekun, wannan karan shiga za muyi, rike da hannun juna, muna masu kallon ruhikan mu. Tsirara. Muraran. Har abada! 


Dec, 2024


Tuesday, 1 April 2025

Batu Kan ‘Tawayen’ Haɗejiyawa: Mahanga.



A ranar goma sha huɗu ga watan Afrilun Dubu ɗaya da ɗari tara da shida (14-04-1906) ne aka yi wannan fafatawar. Tsakani da Allah, ban ma san kiran wannan fafatawar da 'tawaye'. Saboda a gani na ma bai kamata ba. Idan muka yi duba da ita karan kanta kalmar tawayen, za mu ga ai magana take akan tirƙaniya da gwamnatin ƙasa mai mulki ko dai wata tsari dake mulki. 

To da farko dai, Haɗejiyawa ke mulkan kawunansu, duk da akwai turawa a kewayen su da ma cikinsu. Idan aka duba 1903-1905, za a ga cewar duk da an basu damar kafa sansaninsu a waje da cikin Haɗejiyawa, ba su ke mulki ba. To taya za a kira fafatawar da tawaye. Da dai a ce a Katagum, Kazaure, Kano da dai sauran ƙasashen ne hakan ya faru, da za a iya kiran wannan fafatawar da tawaye. 

Yaƙi aka yi. Tsakanin ma su mulkin ƙasar Haɗejiya da Turawan mulkin mallaka. Ba za a kira hakan da tawaye ba. Za dai a iya kiran abun da ya faru da : Gwabzawa, Fafatawa, Yaƙi da dai sauransu. A nan muna kallon haƙiƙanin ma'anar kalmar ce da irin tasirin ta wajen masu karantawa. Da mutum ya ji kalmar tawaye sai ya ɗauka gwamnatin da ke mulki ce a ka yiwa. Alhalin, ita kanta gwamnatin ba ta da iko a ƙasar. Abinda ya sanya su yin haka, ba za dai nace ba— wato dai, abin da ya sa ake kiran wannan gwabzawa da tawaye. 


Shin saboda su turawan sun ci kafatanin ƙasar da yaki ne, banda Haɗejiya, shi ya sa? Ko dan Lugard, wato babban commissioner ya na ikirarin cewar an riga da an ƙwace mulkin ƙasar Hausa? Ko da suka kira hakan da tawaye, mu ba za mu kira shi da hakan ba. Bai ma kamata ba. Kasancewar mu ne masu rubuta tarihin mu. Mu ya kamata muke kiran abun yadda ya kamata. Wannan fafatawa ce. Ta yiwu saboda yadda ta kasance ne shi yasa ka dinga kiranta da tawaye. Amma...

Yadda ‘Gwabzawar’ ta kasance

Sojojin mulkin mallaka sun fara yi wa birnin Haɗejiya ƙawanya ne— sun daɗe da yin hakan— amma bambamcin wannan karan da sauran itace, da nufin yaƙi su kayi. Hakan ya faru ne, saboda sun samu labarin shirye-shiryen masu sarautar haɗejiya wajen yaƙarsu. Saboda sun gaji da yadda suka zama masu alaƙaƙai. Turawan dai sun fara aikawa ne da saƙo, inda suka buƙace su da su bada kai bori ya hau, ko kuma su fuskanci fushin su. Haɗejiyawa kam suka ƙi yarda. Harma an rawaito cewar ɗaya daga cikin baraden Haɗejiya ya mari ɗan aiken. 

To, wasu za suyi mamakin irin wannan Jarunta ka da aka rawaito . Wannan ba komai ba ne Idan muka yi duba ga tasirin Addinin a gwabzawa e. Suna masu yaƙinin cewar ko da an kashe su, sun yi shahada. Saboda haka, a lokacin, ba abin da suke tsoro ko shakka. A mutu ko a yi rai! Hakan kuwa ya faru. Turawan suka samu damar ƙutsawa cikin Haɗejiya. Duk wani ɗan garin, daga matashin zuwa babba — banda tsofaffi da yara mata— suka ɗauki makamai domin gwabzawa. Domin “ba za su yarda da wani kafiri ya mulke su ba. Za su yi jihadi ”

Wannan ya daɗa nuna yadda Haɗejiyawa ke kishin ƙasar su. Da mazajen fama, da ma waɗanda ba su taɓa zuwa yaƙi ba, sai da suka gwabza. Abin mamaki shine, ko da suka ga kayan yaƙin turawa, hakan bai basu tsoro ba ko kaɗan . Ko da suka ga ana kashesu kamar wasu tsaba, suka cigaba da afkawa. A na kashesu, suna ƙara ƙutse. Domin sun san ba su da abin da za su rasa— Suna da yaƙinin yin shahada. 

Amma kuma, sai nake ganin da sun zo da wata dabarar yaƙi da sun ci galaba a kan su. Duk da yike rundunar turawan ma da dama, amma sun fisu sanin ƙasar su. Sun san yadda za suyi su yi nasu wayon. Tunda su turawan sun fisu da kayan yaƙi, su da sai su fisu da dabara. Domin idan akayi galaba a kansu, ko da ba sa raye, abin dai da suke gudu sai ya faru. Da Haɗejiyawa sun sauka daga tunanin shahada kaɗan, sun ɗan karkata tare da mai da dubansu ga mai zai iya faruwa a gaba, da sunyi tunanin hanyoyin da zasu bi wajen ganin sun cimma nasara. An samu kusan shekara uku kafin ‘Gwabzawar Haɗejiya’, wannan wani dama ce suka samu na kintsawa. Ba wai sai da mazantaka kaɗai ba ce a ke samun nasara. Dubara ma wata salon mazantaka ce. 

Wasu lokutan, ana duba ne zuwa ga gaba sannan ayi tanadi. Ba ma wasu lokutan ba, ana so mutum yayi duba zuwa ga gaba a duk lokaci. Da dabaru da salon yaƙi da ba a ci galaba akan su cikin sauki ba. Duk da dai yaƙin ya zo a ƙuraren lokaci, da sarakunan sun shirya masa, da ba a yi irin kisan gillar nan ba. Hakan dai, har wayau, na da nasaba ne da ƙudurin da ke cikin kowannen su, kuma baza na ga laifin su ba dan sunyi hakan. Amma...

Gwabzawar dai ta wanzu tsawon awa biyar ne kacal, kuma an kashe haɗejiyawa kimanin 800-1200 da dawakai sama da ɗari biyar(500). Gaba ki ɗaya manyan masu sarauta (Hakimai), in banda Ciroma da Galadima, sai da a ka kashe su. Hakana Sarkin Haɗejiya Muhammadu Mai shahada, Barori, da Bayi da wasu daga cikin Matayen sarakunan harda ɗaya a cikin matan sarki. Baradai da dama. Mazan fama da dama... Hakan ya faru ne kasancewar Haɗejiyawa ba su zauna sun duba maslahar al'ummar su yadda ya kamata ba. Ba su tsaya sun yi duba iya duba ga wannan lamarin ba. Sai suka kasance masu yin abu ba tare da tsari ba. Hakan kuwa bai hana abin da zai faru ya faru ba. Abin da kowanne su yake gudu sai da ya faru. A kowane lokaci ana buƙatar mutum ya zama mikiya. Ya yi iya ƙoƙarin sa wajen ganin ya duba al'amarin dake gaban sa yadda ya kamata kafin ya yanke hukunci. Ya zamana ya ya yi tsari tun kan abun ya faru. Tsari kuwa ingantacce ba sama-sama ba. Ya tabbatar da kowane sashe ya taɓa, bai bar komai ba. Sai yayi addu'a, ya roki Ubangijinsa da ya taimake sa a yayin da yake mai yin tsarin nan. Dama Allah Yace tashi na taimake ka. Sai bawa ya motsa tukuna kafin Ubangiji ya taimake sa. 

Allāh ya jiƙan zaratan bayin da muka rasa a ƙasar Haɗejiya. Tabbas sun nuna mazantakar da ba lallai mu a yau mu iya ba. Sai dai mu ce za mu ɗan kwaikwaya. Labarin su abin dubawa ne ainun. 

Allāh ya gafarta masu. Ya gafarta wa kusakuransu. Yasa mu zamanto masu koyi da irin tasirin labaran su. Ya sa mu wa'azantu. Mu kasance masu ƙarfafa ƙalmar Sa. Sannan mu kasance masu tsari mai zurfi a dukkannin al'amuranmu.

Ya sa kowanne mu ya zama kamar Mikiya. Amin


Jimrau

February, 2025


Taurari

Taurari sukan kawo mini ziyara a duk sanda na saukar da kai na akan matashi da nufin yin barci. Kowanen su na ɗauke da wani tunani, wani buri da na kasance na taɓa saƙawa. Kamar dai suna so suyi min tuni a tunanin su wai na manta da su. 

Na kan zauna a teburin ƙwaƙwalwata tare da su mu tattauna. Bayani suke yi kan abubuwan da suka ƙunsa. Bayani suke kan rayuwar da suka yi tsakanin lokacin da na kawo su na aje su a cikin ƙwakwalwata zuwa yanzu. Tiryan-Tiryan. Suna masu jeranta mini yadda rayuwar su ta kasance da abin da suke fatar ta zamo. 

Ni dai sauraransu kawai nake dan na san ba su da masaniyar cewar a lokacin da na wassafasu na mance da su. Ba wai dan ba su da faida bane . Ko kaɗan. Sai dai kasantuwarsu a matsayin da suke shi ya fi faida. 

Akwai wani abu mai ƙayatarwa game da mafarkan da ba a riske su ba. Mafarkan da a duk lokacin da mutum ya so zai iya ɗaga hannunsa ya cafko su amma kuma sai ya ƙi. Wannan ƙin. Ƙin yin abin da zai kusanto mutum ga mafarkansa. Wannan ƙin!

So da dama mukan tsai da rayin mu a kan abu guda, ba tare da la'akari da abin da ke zagaye da shi ba. Shin wannan abin yana da ɗanuwa. Mai sunan sa to? Ni dai tunanina, Burikana, Mafarkaina, sun yi tarayya waje guda, kuma shi ne; kasancewar su ababen da suke ƙayatar da duniyar ƙwaƙwalwata

Na cimma su ko ban cimma su ba? Na kusa cimma su? Na fara bin hanyar cimmawa? Duk wannan ba su shafe ni ba. Ko kaɗanna. Ni dai fatana a ce suna nan basu ɓace ba a ƙwaƙwalwata. Iya kasancewar su a nan ya wadatar. Ai mafarkai ne, to me yasa zan so na mayar da su zahiri. 

Gwamma su tsaya a hakan, idan na ɗaga kaina a cikin duniyata na hango su. Su na lulawa samaniyata. Kamar taurari. A cikin taurari. 

Fatana

  Fatana shi ne a ce, ga ni, ga ki, ni da ke, a cikin madafa muna haɗa shayi. Ki ɗan tsoma ganyen na'a-na’a, ni kuma sai na ɗan watsa ka...