Saturday, 17 May 2025

Gare Ki

Wannan saƙo ne da na daɗe ina ta dakon sa. Yau shekaru sama da huɗu kenan rabon da na yi tozali dake, amma a kullum ruhina da ke yake tashi daga barci. Ki na nan sarkafe abin ki. Kina yadda kike so rabin rai. Jiya na jiyo a radio a na ta zabga muhawara kan maza masu kuka, sai dai na murmusa kawai. Ba na ce ba ki taɓa ganin kuka na ba. Kin sha ganinsa, tunda tare muka taso. Ranar da aka haifi ni ma ai kin gani. Amma duk ruwan hawayen da kika gani basa ɗauke da ƙunci sannan basu da ɗaci. Kawai dai ruwan hawaye ne. Ina da yaƙinin cewa kin gani a ranar da muka yi bankwana. Kin ga ruwan ƙwalla na. To amma, wasu lokutan idan na tuna da cewa mutanen da ke zagaye da ni da ɗan dama, sai naji akwai yiwuwar ba ki gane ni ba; ina can ƙurya ko kuma ɗaka, ina ɗauke da hankici ne ko tsumma, bana ce ba nima. Ban iya tunawa ba... Yanzu dai zan ƙaddara cewa baki taɓa ganin ruwan hawayena mai ɗauke da: ƙunci, da-na-sani, kewa, bege, da so ba. 

Abin da kuwa ma ba ki sani ba shine, wannan ne lokaci na ƙarshe da irin wannan hawaye ya tsatso daga gulbin idanuwana. A duk lokacin da na ji ƙwalla na kan so na ji ya ya yake. Kamar kullum dai babu komai a cikinsa. Ba shi da bambanci da ruwan sha. Ruwan rijiya. Kai hatta ma garɗinsa babu wasu ta’ajibbai da ke kewaye da shi. Hakan kuwa yasa ma na daina kukan. Saboda na san koda na yi sa, ba ya ɗauke da wannan garɗin. Wannan ɗanɗanon da na taɓa riska.

Sahiba, kin tafi da wani ɓari na rayuwata da babu mahalukin da zai iya kawo madadinsa. Ƙunci wani abu ne mai ɗaci, amma ya zauna a wani lungu a ruhina ya yi min kane-kane. A ɓoye yake mulkinsa, ta hanyar amfani da wasu shauƙin can daban wajen isar da saƙon sa. Misali, yanzu sai na ji farin ciki ya mamaye ni haka kurum, idan ko nai ƙuri, sai na ga ashe ba farin cikin kaɗai nake ba — shi ne kaɗai ya bayyana; akwai wani abu mai duhun launi a can ƙurya a zaune yana mai kallona, yana murmushi tare da gyaɗa kansa. 

Na kan ji wani ƙara a cikin ruhina wasu lokutan, koda na duba, sai na ga tana fitowa ne daga wani saƙo a can cikin ruhina. Ƙarar dai ba ta da ƙara. Shiru ce ma. Kawai tsabagen shiru ne ya sanya ƙarar fitowa. Wato dai a can cikina akwai wani irin rami kamar holoƙo da babu komai a cikinsa sai shiru. Ban ma ziyarar sa saboda tsoro da fargabar abin da zan buɗe na gani. E, ƙwarai, ni matsoraci ne, ban son ziyarar in da zai kai ni kushewa. Har yanzu ina da muradai da burika dana ke fatan cimmawa, watarana. Na san idan na shiga wannan rami kam da matsala. Ina gujewa matsala duk da yake dai ba zana iya guje masa ba, sahiba. Wannan ramin kushewarmu ne, a nan na binne soyayyarmu. A nan nake fata wata rana kurwata zata shige dan ta sadu dake.

Sai dai kuma ina rayuwa tamkar ba kya tare dani; tamkar babu ɓurɓushinki a komai na; tamkar iskar da nake shaƙa iska ce kawai, ba sinadaran hazon ruhinki ba; tamkar zuciyata na ci gaba da bugawa ne ba tare da taimakonki ba; tamkar rayuwata — a yanzu — ba wanzuwa take a doron tunaninki ba. Tamkar ba ki, sai dai kuma akwai ki a komai na, Sahiba. Tamkar ba ki, sai dai a duk sanda na tuna wane ni — mantawa nake wasu lokutan — ina ganin ki a samana kina mai kallona. 

Wannan abun, wani lokaci, na ci min rai ƙwarai amma da zaran na tuna cewa duk abubuwan da na lassafta a baya, kina da tasiri a gare su, kuma gaskiya ne, ke ɗin ce sinadarin rayuwata, sai na ji sanyi a ruhina. Sanyin na zuwa ne daga gun ki sahiba. Ai da ma kece mai sanyaya mini zuciya. 

A duk lokacin da na yi koda tunanin cewa kina nesa dani sai ruhina ya gargaɗe ni, domin wai zunubi ne mai girma faɗin haka. Wai kina kusa dani fiye da kusancin jijiyoyi ga ɗan Adam. Kuma haka ne fa, ko? Tunda dai ina tunawa da ke a duk sakan da duk minti. Barci ne kawai ke hanani tunawa dake, kuma ai wasu lokutan ina mafarkinki: wai gamu a wani dausayi; ni dake, da ƙaunar mu, muna masu kallon ruhikan mu ba tare da magana ba, akwai murmushi a saman fuskar mu sannan akwai alamar cikar aminci a kowannenmu. Ina sonki, sahiba. Ina tsananin kewarki. 

A nan alƙalamina — da na sato — ya ƙare daƙushewa, kin fini sanin iya adadin kewarki da nake yi. Kin fini sanin iya nauyin begenki da ke a ruhina. Kin fini sanin cewa ina sonki. Saboda haka, wannan rubutun duk domin ni na yi shi. Ke fa ba kya buƙatar sa — kina ganin gaskiya a can inda kike, saboda haka, kin fini sani. 


April,2024

No comments:

Post a Comment

Matafiyan Tsuntsaye

Akwai mutanen da suka kasance kamar tsuntsaye matafiya; sukan shigo rayuwar mutum lokaci guda — na lokaci ƙalilan. Kamar matafiyan tsuntsaye...