Taurarin Samani
Ba kasafai nake samun kaina a cikin yanayin kaɗaici ba saboda a duk lokacin da na ɗaga kaina na yi duba zuwa ga samani, akwai ababen da ke fitowa daga duniyar tunanina dake ƙayatar da ni. Akwai so, misali. Ina son sa, ina son na yi ta kallon sa. Haka kurum, ba wai don ina so na kasance tare da shi ba ne, ko kusa — wasu abubuwan ganin su daga nesa ya fi, kuma akwai tazara mai yawa tsakanin duniyar tunanina da ta zahirina. Akwai kuma kyawu. Zan iya cewa kusan duk ababen da ke ƙayatar da ni akwai kyawu a cikinsu. Misali, dubi shayi; dubi turirin da ke ziryowa sama daga moɗar shayi; dubi sinadaransa; dubi guminsa da ke jikin shatin moɗar; dubin zatinsa shi karan-kan-sa; Akwai kyawu a shayi da kominsa!
Akwai kuma tarihi, wanda ya kasance mai kawo mini ziyara duk daƙiƙa. Kusan komai na yi, sai na ga ɓurɓushin tarihi a cikinsa. Ballantana, a duniyar tunanina, inda: zamanin da-da ke artabu da zamanin da, masana fikirar da ke artabu da na yanzu, tutar masarautun Hausawa ke artabu da ta Fulani, Gobirawa ke ci gaba da kawo hare-hare Sakkwato da Zamfara, Katsinawan Maraɗi ke kawo sumame Katsina, Buharin Haɗejiya ke bawa daular Sakkwato wahala, musayen zazzafar rubututtuka tsakanin El-kanemi da Muhammadu Ɓallo ke cigaba da kwaranya, Kanawa ke tarbar Sarkinsu Alu bayan Basasa: shi a saman doki, sanye da fararen kaya, mayaƙa a bayansa — bayansa ma a bayansa. Marubuta ke ci gaba da rubutu ba tare da damuwa da duk wannan ba; Sarkin Musulmin da ke shiga ɗaka ya fara rubuta waƙe bayan ya gama fille kan maƙiya. Matar so, ma'abociyar ilimi, Nana Asma'u da ke ciyar da al'umma gaba ta hanyar koyar da su daga ƙoramar iliminta.
A duk wannan, sai kuma kaga ababen sun rikiɗe sun zama ayar tambaya: “Shin a wani ƙarni nake a duniyar tunanina? A wani zamani nake? Shin kasancewata a wani ƙarnin na da tasiri kan rayuwata ta yau da kullum ko ƙa-ƙa?”
Tambayoyin sai su rikiɗe su zama wata mata, kyakkyawa mai cikar zati da kamala. Ba ta da ko da lulluɓi amma zatinta ya zame mata lulluɓi. A fuskarta akwai wani tabo baƙi mai kama da ɗigon tawada, tana murmushi kuma ta ɓata rai wasu lokutan, ta kalle ni sai kuma ta yi kamar ba ni. Da na yi ƙuri ina dubanta sai na lura da hannunta akwai zanen tambarin arewa a manne a saman tafukanta. Gefe guda kuma a rigarta — can samanta, kusa da wuyarta, ɗan kasa kaɗan — akwai zanen gidan da babu komai a ciki. A gefenta akwai littafan da babu koda ɗigon tawada ciki. Sannan akwai dokin da ba ta hawa sai dai kullum a yi ta mata ado.
Sai kuma ta rikiɗe ta zama ni. Kamar ni kamar ba ni ba. Ga ni nan da littafai tuli ina ta nazarin su, ga maguna a gefe na manya-manya masu gashi mai laushi da daɗin taɓawa. Farare dukkaninsu. Ga moɗar shayi ina ta sha ina ta kamfata—na gama sanin tarihi—na kafa tarihi. Ina ta murna sai kuma na fara kuka. Kamar dai yadda akwai tarin alheri ga sani, haka ma akwai nakasu ga yawan sani: ga ni nan a wani tsibiri, a zagaye da ni Teku da Bishiyoyi. Sai hadari ya haɗe lokaci guda daga ko’ina. Ina jin ƙishi ina ta jiran ruwan domin na sha. Sai ɗigo ɗaya ya fito daga gajimaren, yai ta juyi har ya iso duniyar tamu har ya faɗa tekun. Da ina ta murna yanzu kuma na fara kuka. Shin ku faɗa min, na sani ne ko kuma ban sani ba? Saboda duk yadda kuka duba, dole ne na koka — ban ɗanɗana ɗigon ba, ba zan iya sha daga tekun ba. Yanzu dai neman ruwa ya kama ni— ko dai na je nemansa ko kuma na zauna na jiraye ruwan sama.
Sannan akwai adadin kwanaki da shekaru da na ɗiba a duniya, da yadda ma na yi amfani da su. Guje-gujen da na yi da ma kura-kuran da na tafka. Kuma ban da-na-sanin kurakurai na ko kaɗan. Kallon su ma nake ina murmushi a raina. Ba wai saboda na amfana da su ba ne — e ƙila, tabbas ma na amfana da su — illa don kasancewar su kurakurai shi ya sa na ke murmusawa a gare su. Ni gani na nake a cikinsu; ni a mutum ba a halittar da na ƙera wa kaina ba. Ni a gangariyar mutum mai kuskure. Mutum ajizi. Shi ya sa na ke murmushi, don a kullum suna tuna mini da waye ni idan na zama mai mantuwa— saboda mantuwa halittace da aka yi ta don mu.
Mantuwa na da tasiri ƙwarai a wannan bigire saboda ni dai ba komai nake iya tunawa ba. Misali, ba zan iya tuna ababen da suka faru da nake shekara 10-15 ba, sai dai ƴan kaɗan daga cikin abubuwan da suka wakana. Na san na yi rashin lafiya a waɗannan shekaru, sannan na nuna hazaƙa kwarai a makaranta. Sannan zan ɗan iya tuna abokaina da wasu abubuwan da suka faru da ni kaina. Waɗannan duk ba su kai kaso goma cikin ɗari daga ciki ba. Mantuwa na da daɗi. Har fuskoki ma ina mantasu, ina manta yadda duniyata ta kasance a baya, ina manta waɗanda suka munana min da ma waɗanda suka taimaka min na tsallaka titi. Waɗanda suka zage ni da ma waɗanda suka yabe ni. Tabbas mantuwa na da daɗi!
Akwai kuma gulbin tunani da ke cigaba da cika kamar a tsakiyar damuna. Zan iya riskar komai a duniya ta hanyar tunani. Ina shagala ƙwarai a wannan yanayi, duk da yake dai, da tunani nake tunanin, amma hakan ba ya hana ni samun cikakkiyar annashuwa a yayin yinsa. Ina farin ciki ƙwarai a wannan dausayin, ina kasancewa tatil tamkar wanda ya kwana a buge tsabar farin ciki. Ko dai tunanin ne ke bugar da ni ko kuma kasancewar na san ina tunanin ne, ba na ce ba. Misali, zan iya tunanin cewa ni ina tunanin abu kaza da kaza sun faru a gare ni, yayin da nake a mace ko a raye. Tunanin ba sa damuwa da kasancewa ta a mace, su ko a jikinsu. Kawai za su cigaba da tafiya ne bisa tsarin da ruhina — ƙila — ya tsara musu. Hakan kuwa na burge ni matuƙa kuma ina samun biyan buƙata — duk da ba ni ba ne nake tsara su, zuwa suke. Biyan buƙatar kuwa da nake samu ba ya wuce kasancewar ina iya sanin abin da zai wakana da raina ko babu. Hakan na matuƙar ƙayatar da ni. Duk da yake, wasu lokutan, ina jan ragamar tunanin zuwa in da nake so su je — saboda zan iya hakan kuma ina da ikon yi hakan, tunda tunanina ne bana kowa ba! Ina matuƙar son wannan ɓarin na duniyar tunanina. Ban son me ya sa ba, amma ina jin, ƙila, saboda ni ne mai yinsu ba kowa ba.
Hakazalika, duk a nan duniyar, na kan samu kaina a wani yanayin da ke sani tunano duk abubuwan da suka faru, da waɗanda za su faru, da waɗanda nake so su faru, da waɗanda nake fatan su faru, da waɗanda nake hanƙoron faruwar su, da waɗanda haka kurum suke faruwa. Iya wannan na iya kaini duk wani irin bene na farin ciki da ɗan adam zai iya kintatawa. Idan ma kintacen za ya kai can sama-saman-samaniya ne, to ni ma farin ciki na na wurin, tare da....
Ka da ku bi ta zancena, kawai ina labarta muku kaɗan ne daga cikin ababen da ke shigowa duniyata da zaran na ɗaga kayina ko ruhina na kalli sama. Da zaran na kaɗaitu, da zaran yanayin shiru ya riske ni. Shi ya sa nake son barci. Amma fa, hakan ba ya hana ni ƙin shiru, saboda a wasu lokutan — a gaskiya, lokuta masu yawa — nakan riski aminci a wannan yanayi. Shi ya sa nake son shiru. Kuma ina son barci. Kuma ma ina son tunani — saboda suma da hular shiru suke zuwa, matayensu kam da kalabinsa, aworworansa, mayafinsa, murmushinsa, kyawunsa.
Kai ina son shiru! A halin yanzu ma a can wata ƙasa nake a duniyar tunanina, ina zaune a dandamalin rayuwa ina mai kallonta, a samana akwai bishiyar Ɓaure mai ganyayen koraye da cikar rassa. A gefena akwai moɗar shayi. A can gaba na kam akwai kyakkyawar budurwa mai cikar zati, ni kuwa sai kallonta nake: ina shan shayi, ina ta son shiruna!
08/05/25
No comments:
Post a Comment