Wednesday, 16 July 2025

Da Kuma Akwai Wannan Lumanar Da Ba Za A Iya Fasalta Wa Ba


Da akwai wannan lumanar da bawa kan riska yayin da ya tsinci wannan littafin da ya yi shekaru yana nema a wata ƙurya a cikin ma'adanar taliffai. Duk yadda wannan bawan zai yi kuwa, ba zai iya sa ta a gurbin da ya dace da ita ba.

Ko da zai ce: ya ji wani abu a cikinsa tamkar an kuma haihuwarsa. Ko kuwa: zuciyarsa ta fid da fuka-fuki ta lula samani inda ta zauna tare da rana har ta narke. Ta gwauraye da iska. Ta zama marar nauyi. Ta tsaya cak. Ta yi ta ruri, gunji, tana neman mafari. Ko da zai ce: ya kasance tamkar lokacin da aka halicce sa — kafin a sanya so a cikinsa; kafin ransa ya samu hankali. Wannan lumanar da ya riska tsakanin hankali da rashin hankali. 

Ko: ya ji kamar ya mutu baicin yana raye; kamar duniya kowa ya mutu sai shi kaɗai; kamar a samaniyar ma babu giza-gizai; kamar farin cikin mahaifiyarsa lokacin da ya fara kiranta da ‘Mama’; kamar irin walƙiyar da ya bayyana a idaniyarta a san da ya fara ta-ta-ta. Irin tagomashin da ke wanzuwa yayin kallon fuskar masoyiya. Irin yabanyar da ke fitowa daga ƙalbi a yayin kallon murmushin masoyiya. Irin macewar da rai ke yi a lokacin da ya ji ƙamshin turaren masoyiya.

Ko ko ma: ya ji tamkar matalaucin da ya riske alatu a kogo, ko kuwa ma mai karayar arziƙin da arzuƙansa suka dawo. In ya so ya ce: ya ji kamar yaron da ya soma ɗanɗanar romon ilimi: garɗin sa, zaƙin sa, mai yawan sukari. Annashuwar da ke ɗarsuwa a rai idan ya amsa tambaya daidai; Iskar da ke wantagaliliya da kafatanin tunaninsa a yayin da ake tafa mai; rijiyar shauƙin da ke ta amayar da wuta a maimaikon ruwa; yanayin da ya tsinci kansa a lokacin da rayuwa ta lasa masa zauƙin da ke a miyar ilimai.

Duk waɗannan ba za su bayyana iya girman yanayin da ya shiga ba. Duk waɗannan ba za su haska wa makaranci iya tumbatsar da ɗan ƙaramin dunkulen da ke a ƙirjin bawan nan ke yi ba. Duk waɗannan sai dai su kwatanta wa mai karatu iya budum-budumar da bawan nan ya yi a cikin kogin farin ciki.

Kuma ya tsinci kansa a wannan yanayin ne a wata ƙurya, wadda haske bai wadata ta ba, wadda ƙura ce ke ƙawata ta, wadda aka daɗe ba a leƙa ta ba. A can wani ɗan ƙaramin ɗaki mai ɗauke da tulin litattafai.

08/07/25

Wednesday, 2 July 2025

Sihirtacciyar Salka


Akwai wasu halittu da ke nasarar killace rai a matsayin ruwa su sa shi a salkarsu. Su ba sha za su yi ba, ba kuma fito da ran za su yi ba har sai sun kai madakatarsu. Sai su zubar da ruwan walau a ƙasa ko a cikin randar gidansu. Idan ya ci sa'a suka saka shi a randar, to ba ƙaramin farin ciki zai yi ba, saboda ko ba komai: zai sirku da ruwan gidansu, za su tsotsa daga sinadaransa, zai kuma dinga jin sautin muryarsu, da ma ƙamshin turaren su. Zai kuma shige can cikinsu. Zai iya tagomashi da sirrikan da ke kwance a cikinsu.

Idan kuma watsar da ruwan suka yi a ƙasa, sai ya yi ta ratsa yashi da tsakwankwani; tsutsosi da ƙananun halittu; aljanu har ma da ɓurɓusan ƙasussan bil'adama da dabobbi; ƙasashen zamanin da da ƙasa ya rufe; kududdufai da ma’adanar kayayyakin alatu; har ya isa inda zai haɗu da sauran rayuka kamar sa, inda suke zaune a daira, ƙafafun kowannensu a tankwashe. Suna masu karatu daga wani littafi — mai kama da littafin so.

Abin mamaki kuwa, duk cikinsu, babu wanda ya san sunan halittar da ya haɗu da. Babu wanda ya damu ya san sunanta. Kawai makillaciyar ransu ce suke so, ita ɗin da ba ta da suna.

Su kuma waɗannan halittun ba su ma san da sun yi hakan ba. Ƙila murmushi suka yi kawai, ba su san da cewa a take rai ya narke ba; saboda zafin wannan murmushin a gare sa. Saboda tsananin farin cikin tozali da wushiryar makillaciyar ransa. 

Ƙila kuma kallon sa suka yi da waɗannan idaniyar ta su, wandararru, masu kama da rana a tsakiyar sahara, sai ransa ya fara amon wutar ƙaunar wannan idaniya; ya kasance mai fata ya zama ko da ruwan idaniyar ne — sai kuma ya zama! Amma maimakon ya ƙare a idanunta sai ya gan shi a salkarta. Amma kuma ita ke riƙe da shi a hannunta. Hakan ya wadatu a gare sa!

Ƙila kuma kiran sunansa ta yi, sai kawai ya ga ransa ya fara fiddo da fuka-fukai. Ransa ya zama kamar wani mala'ika. Ya yi ta harbawa sama har ya cimma zara ya zauna a bisanta. Sai ya narke. Sai ya zamo ruwa. Ya sulalo daga sama ya shige cikin salkarta.

Akwai wasu halittun da ke ƙona rai, su narkar da rai, su zuzuta rai, su haukatar da rai, su kuma makantar da rai. Yadda suke so — duk da yake ba lallai da sonsu ba, amma shi rai bai damu da wannan ba.

Akwai waɗannan halittun a ko'ina. Kuma a koyaushe idan na haɗu da su, sai na zame ɗaya daga cikin nau'kan ruwan salkarsu. 


17/06/25

Saturday, 14 June 2025

Matafiyan Tsuntsaye


Akwai mutanen da suka kasance kamar tsuntsaye matafiya; sukan shigo rayuwar mutum lokaci guda — na lokaci ƙalilan. Kamar matafiyan tsuntsaye, sukan yi sheƙarsu a rayuwar mutum su yi ta rera masa waƙoƙi — su warkar da ciwukan zuciyar da ya addabe sa, su gyara masa rayuwarsa. Abubuwan da ba ya yi sai ya fara; idan ya faɗi su tayar da shi, idan ya kuskura hanya su dawo da shi bisa tafarki, idan ya nemi shagala su watsa masa ruwa don ya tashi. Idan ya nemi ya ɓata, su nuna masa hanya, duk ta hanyar waƙoƙinsu, waɗanda suke rerawa a kodayaushe. 

Kamar matafiyin tsuntsu, sai ya yi tafiyarsa ya bar sheƙar a saman bishiyar. Babu kowa dai a kai, amma a duk lokacin da mutum ya ɗaga kansa sama, zai hango gidan wannan tsuntsun da ya sauya masa rayuwa. Ba lallai ya kuma dawowa ba, ya tafi kenan. 

To haka Malam Jamilu ya zame wa rayuwata. A daidai lokacin da na gaza gane ina na dosa, sai ya yada zango a bisa bishiyata, ya yi ta rera mini waƙoƙin adabi, tarihi, da wasullan Hausa. Ya yi ta ciyar dani daga tsirran ƙasar Hausa. Idan na kishingiɗa ya taso ni, yace mini na je na nemo masa ciyayi domin mu tada baƙi. Neman ciyayi kam dama na bani wuya, amma duk da haka bai saduda ba. Akwai fa bishiyu da dama a wannan jejin, amma ni kaɗai ya horar fiye da misali. Ni kaɗai nake jin haka — kusan kowa yana sauraren waƙoƙinsa kuma yakan aike su domin su nemo ciyayin. 

A lokaci ƙalilan, bishiyata ta fara rassa, da kaɗan, da kaɗan furarruka suka fara fitowa. Sai dai an ɗau tsawon lokaci kafin bishiyar ta fara ƴaƴa. Lokacin ya bar shingen mu. Idan ma yana dajin baya kusa damu. Ni kuma saboda wautata sai na mance da shi, na ƙi na biɗesa. Na ƙi na tambayi ƙwari da tsutsosin da ke ƙarƙashin ƙasa ko sun taɓa ganinsa. 

Yau dai bishiyar ta fara ƴaƴa — haka nake tunani. To saidai, ashe ba zai taɓa riskar ƴar bishiyar da ya raina ba da kansa. Yar bishiyata da ya rera wa waƙe, ƴar bishiyar da ya zame wa fitila a cikin duhun dare. Yau ba zai gansu ba, yau ba zai taɓa dawowa bisansu ba. Ya tafi kenan, ashe ba zai kuma dawowa ba. 

Akwai mutanen da suka kasance kamar matafiyan tsuntsaye: sai su haskaka alƙaryar mutane da zatinsu, su yi ta shawagi a bisansu, su ƙayatar da duniyarsu. Sai kuma su tafi, za su dawo? Ƙila.... Wasunsu kuma sun tafi kenan. Sheƙarsu na nan dai, hakana tasirin su ga rayuwar mutanen alƙaryar. 

Irin waɗannan mutane ba sa mutuwa, ko sun mutu da akwai ɓurɓushinsu a jikin kowanne. Da akwai baitukan waƙoƙinsu a dashe a ƙalbin mutane. Da akwai ƙarin harshensu a bakunan mutane. Da akwai garɗin koyarwarsu a dasashi da ma saiwar bishiyoyi. Kogunan alƙaryar kam za su ci gaba da ɗaukar wasulla da baƙaken da suka taɓa suɗaɗowa daga waƙoƙinsu. Irin waɗannan mutane na rayuwa har abada. Irin waɗannan mutane ba sa mutuwa.

Allāh Ka gafarta wa bawanKa; Ya kasance kamar matafiyin tsuntsu ne a ban ƙasa. Kai ne Majiɓincinmu, Kai ne Mai rahama a garemu. RahamarKa ta baɗe ko'ina. RahamarKa na da tasiri akan kowa. Ka sanyaya masa yadda ya sanyaya mana. Ya yi iya nasa ƙoƙarin wajen kula da bayinKa; wajen ciyar da halittarKa; wajen ɗanɗana wa al'ummarKa daga ilimin da Ka tsam masa; Ka sa ya zama mai ƙwanƙwaɗa daga tafkin rahamarKa, don, koda ƴar ɗigo ya samu, ta wadace shi har abada. Allāh Ka gafarta wa Malam Jamilu, mutum ne salihu da bai son fitnu, ka buɗe masa ƙofofin rahamarKa, domin, ya kasance mutum ne mai kyawawan ɗabi'u.

Marigayi Malam Jamilu (d. June 2025)



Monday, 9 June 2025

Yawon Duniya

Masoyiya, shin za ki iya shimfiɗa 
Mini tabarma a wani sashe na 
Zuciyar ki don na zamna?
 
Ƙafufuwana sun gaji da 
Taku a cikin zuciyarki 
Babu dare, babu rana.

Ba lallai sai kin samo 
Kilishi ba ko kujerar 
Nan mai taushi da laushi.

Kawai soyayyarki nake so 
Ta zame mana tabarma; 
Ni a gefe ɗaya, ke a ɗaya.

Ta ja mu, ta ɗaga mu, ta lula mu:
Mu keta gajimare; mu ratsa ta 
Gangamin tattabaru; mu wuce sinadaran
Numfashi; mu lula mu tafi can inda cida 
Ke koyan tashi. Daga nan, ƙila, 
Sai mu garzaya duniyar taurari;
Mu faɗa kogin da ke bisansu, mui wanka, 
Mu sauya buƙatu, mu kaifafa muradai;
Mu tsaftace soyayyarmu.

A cikin zuciyarki, da zaki yarda, 
Da sai na janyo tabarmar nan bakin teku. 
Mu zamana muna kallon shirgawar 
Kifaye mu kadanmu 
Sai kuma teku.

Da zaki yarda, da sai na baza 
Komata don na kamo kifayen 
Da ke cikinai, kowannensu, na 
Buɗe cikinsu, inda ƙoƙon lu'ulu'u 
Mai ɗauke da soyayyarmu 
Ke ciki a ɓoye.

Masoyiya, so nake kawai na samu 
Aminci a cikin zuciyarki; ki ɗan lasa 
Mini daga tekun ƙaunarki; ki ci gaba 
Da alkinta mana soyayyarmu a cikin 
Ƙokon lu'ulu'u nan mai haske. 
Ƙila wataran, idan muka ƙare 
Yawon duniyar mu, zamu shiga 
Domin mu ga iya girmanta. 

Saturday, 17 May 2025

Gare Ki

Wannan saƙo ne da na daɗe ina ta dakon sa. Yau shekaru sama da huɗu kenan rabon da na yi tozali dake, amma a kullum ruhina da ke yake tashi daga barci. Ki na nan sarkafe abin ki. Kina yadda kike so rabin rai. Jiya na jiyo a radio a na ta zabga muhawara kan maza masu kuka, sai dai na murmusa kawai. Ba na ce ba ki taɓa ganin kuka na ba. Kin sha ganinsa, tunda tare muka taso. Ranar da aka haifi ni ma ai kin gani. Amma duk ruwan hawayen da kika gani basa ɗauke da ƙunci sannan basu da ɗaci. Kawai dai ruwan hawaye ne. Ina da yaƙinin cewa kin gani a ranar da muka yi bankwana. Kin ga ruwan ƙwalla na. To amma, wasu lokutan idan na tuna da cewa mutanen da ke zagaye da ni da ɗan dama, sai naji akwai yiwuwar ba ki gane ni ba; ina can ƙurya ko kuma ɗaka, ina ɗauke da hankici ne ko tsumma, bana ce ba nima. Ban iya tunawa ba... Yanzu dai zan ƙaddara cewa baki taɓa ganin ruwan hawayena mai ɗauke da: ƙunci, da-na-sani, kewa, bege, da so ba. 

Abin da kuwa ma ba ki sani ba shine, wannan ne lokaci na ƙarshe da irin wannan hawaye ya tsatso daga gulbin idanuwana. A duk lokacin da na ji ƙwalla na kan so na ji ya ya yake. Kamar kullum dai babu komai a cikinsa. Ba shi da bambanci da ruwan sha. Ruwan rijiya. Kai hatta ma garɗinsa babu wasu ta’ajibbai da ke kewaye da shi. Hakan kuwa yasa ma na daina kukan. Saboda na san koda na yi sa, ba ya ɗauke da wannan garɗin. Wannan ɗanɗanon da na taɓa riska.

Sahiba, kin tafi da wani ɓari na rayuwata da babu mahalukin da zai iya kawo madadinsa. Ƙunci wani abu ne mai ɗaci, amma ya zauna a wani lungu a ruhina ya yi min kane-kane. A ɓoye yake mulkinsa, ta hanyar amfani da wasu shauƙin can daban wajen isar da saƙon sa. Misali, yanzu sai na ji farin ciki ya mamaye ni haka kurum, idan ko nai ƙuri, sai na ga ashe ba farin cikin kaɗai nake ba — shi ne kaɗai ya bayyana; akwai wani abu mai duhun launi a can ƙurya a zaune yana mai kallona, yana murmushi tare da gyaɗa kansa. 

Na kan ji wani ƙara a cikin ruhina wasu lokutan, koda na duba, sai na ga tana fitowa ne daga wani saƙo a can cikin ruhina. Ƙarar dai ba ta da ƙara. Shiru ce ma. Kawai tsabagen shiru ne ya sanya ƙarar fitowa. Wato dai a can cikina akwai wani irin rami kamar holoƙo da babu komai a cikinsa sai shiru. Ban ma ziyarar sa saboda tsoro da fargabar abin da zan buɗe na gani. E, ƙwarai, ni matsoraci ne, ban son ziyarar in da zai kai ni kushewa. Har yanzu ina da muradai da burika dana ke fatan cimmawa, watarana. Na san idan na shiga wannan rami kam da matsala. Ina gujewa matsala duk da yake dai ba zana iya guje masa ba, sahiba. Wannan ramin kushewarmu ne, a nan na binne soyayyarmu. A nan nake fata wata rana kurwata zata shige dan ta sadu dake.

Sai dai kuma ina rayuwa tamkar ba kya tare dani; tamkar babu ɓurɓushinki a komai na; tamkar iskar da nake shaƙa iska ce kawai, ba sinadaran hazon ruhinki ba; tamkar zuciyata na ci gaba da bugawa ne ba tare da taimakonki ba; tamkar rayuwata — a yanzu — ba wanzuwa take a doron tunaninki ba. Tamkar ba ki, sai dai kuma akwai ki a komai na, Sahiba. Tamkar ba ki, sai dai a duk sanda na tuna wane ni — mantawa nake wasu lokutan — ina ganin ki a samana kina mai kallona. 

Wannan abun, wani lokaci, na ci min rai ƙwarai amma da zaran na tuna cewa duk abubuwan da na lassafta a baya, kina da tasiri a gare su, kuma gaskiya ne, ke ɗin ce sinadarin rayuwata, sai na ji sanyi a ruhina. Sanyin na zuwa ne daga gun ki sahiba. Ai da ma kece mai sanyaya mini zuciya. 

A duk lokacin da na yi koda tunanin cewa kina nesa dani sai ruhina ya gargaɗe ni, domin wai zunubi ne mai girma faɗin haka. Wai kina kusa dani fiye da kusancin jijiyoyi ga ɗan Adam. Kuma haka ne fa, ko? Tunda dai ina tunawa da ke a duk sakan da duk minti. Barci ne kawai ke hanani tunawa dake, kuma ai wasu lokutan ina mafarkinki: wai gamu a wani dausayi; ni dake, da ƙaunar mu, muna masu kallon ruhikan mu ba tare da magana ba, akwai murmushi a saman fuskar mu sannan akwai alamar cikar aminci a kowannenmu. Ina sonki, sahiba. Ina tsananin kewarki. 

A nan alƙalamina — da na sato — ya ƙare daƙushewa, kin fini sanin iya adadin kewarki da nake yi. Kin fini sanin iya nauyin begenki da ke a ruhina. Kin fini sanin cewa ina sonki. Saboda haka, wannan rubutun duk domin ni na yi shi. Ke fa ba kya buƙatar sa — kina ganin gaskiya a can inda kike, saboda haka, kin fini sani. 


April,2024

Wednesday, 7 May 2025

Taurarin Samani


Ba kasafai nake samun kaina a cikin yanayin kaɗaici ba saboda a duk lokacin da na ɗaga kaina na yi duba zuwa ga samani, akwai ababen da ke fitowa daga duniyar tunanina dake ƙayatar da ni. Akwai so, misali. Ina son sa, ina son na yi ta kallon sa. Haka kurum, ba wai don ina so na kasance tare da shi bane, ko kusa, wasu abubuwan ganin su daga nesa yafi, kuma akwai tafiya mai tsawo tsakanin duniyar tunanina da ta zahirina. 

Akwai kuma kyawu, zan iya cewa kusan duk ababen da ke ƙayatar da ni akwai kyawu a cikinsu. Misali, dubi shayi, dubi turirin da ke ziryowa sama daga moɗar shayi, dubi sinadaran sa, dubi ƙwallar sa dake jikin shatin moɗar, dubin zatin sa shi karan-kan-sa. Akwai kyawu a shayi da kominsa....

Akwai kuma tarihi: wanda ya kasance mai kawo mini ziyara duk sakan. Kusan komai na yi, sai na ga ɓurɓushin tarihi a cikinsa. Ballantana, a duniyar tunanina, inda: zamanin da-da ke artabu da zamanin da, masana fikirar da ke artabu da na yanzu, tutar masarautun Hausawa ke artabu da ta Fulani, Gobirawa ke ci gaba da kawo hare hare Sakkwato da Zamfara, Katsinawan Maraɗi ke suɗaɗowa Katsina, Buharin Haɗejiya ke bawa daular Sakkwato wahala, musayen zazzafar rubututtuka tsakanin El-kanemi da Muhammadu Ɓallo ke cigaba da kwaranya, Kanawa ke tarbar Sarkinsu Alu bayan Basasa — shi a saman doki, sanye da fararen kaya, mayaƙa a bayansa, bayansa ma a bayansa. Marubuta ke ci gaba da rubutu ba tare da damuwa da duk wannan ba, Sarkin Musulmin da ke shiga ɗaka ya fara rubuta waƙe bayan ya gama fille kan maƙiya. Matar so, ma'abociyar ilimi, Nana Asma'u da ke ciyar da al'umma gaba ta hanyar koyar dasu daga ƙoramar iliminta. 

A duk wannan, sai kuma kaga ababen sun rikiɗe sun zama ayar tambaya: shin a wani ƙarni nake a duniyar tunanina? A wani zamani nake? Shin kasancewata a wani ƙarnin na da tasiri kan rayuwata ta yau da kullum ko ƙa-ƙa? 

Tambayoyin sai su rikiɗe su zama wata mata, kyakkyawa mai cikar zati da kamala. Ba ta da ko da lulluɓi amma zatin ta ya zame mata lulluɓi. A fuskar ta akwai wani tabo baƙi mai kama da ɗigon tawada, ta na murmushi kuma ta ɓata rai wasu lokutan. Ta kalleni sai kuma ta yi kamar ba ni. Da nai ƙuri ina dubanta sai na lura da hannunta akwai zanen tambarin arewa a manne a saman tafukanta. Gefe guda kuma a rigarta— can saman ta, kusa da wuyarta, ɗan kasa kaɗan— akwai zanen gidan da babu komai a ciki. A gefenta akwai littafan da babu rubutu a can ciki. Sannan akwai dokin da bata hawa sai dai kullum ayi ta mata ado. 

Sai kuma ta rikiɗe ta zama ni. Kamar ni kamar ba ni ba. Ga ni nan da littafai tuli ina ta nazarin su, ga maguna a gefe na manya manya masu gashi mai laushi da daɗin taɓawa. Farare dukkansu. Ga moɗar shayi ina ta sha ina ta kamfata. Na ƙare sanin tarihi—na kafa tarihi! Ina ta murna sai kuma na fara kuka. Kamar dai yadda akwai tarin alheri ga sani hakama akwai nakasu ga yawan sani. Ga ni nan a wata tsibiri, a zagaye da ni Teku da Bishiyoyi. Sai hadari ya taso daga ko'ina. Ina jin ƙishi ina ta jiran ruwan domin na sha. Sai ɗigo ɗaya ya fito daga gajimaren, yai ta juyi har ya iso duniyar tamu har ya faɗa tekun. Da ina ta murna yanzu kuma na fara kuka. Shin ku faɗa min, na sani ne ko kuma ban sani ba? Saboda duk yadda kuka duba, dole ne na koka: Ban ɗanɗana ɗigon ba, ba zan iya sha daga tekun ba. Duk sauran dalilan daga baya ne fa. Yanzu dai neman ruwa ya kama ni— ko dai na je nemansa ko kuma na zauna na jiraye ruwan sama. 

Sannan akwai adadin kwanaki da shekaru da na ɗiba a duniya, da yadda ma na yi amfani da shi. Gujegujen da na yi a nan da ma kurakuran da na tafka. Kuma ban da-na-sanin kurakurai na ko kaɗan. Kallonsu ma nake ina murmushi a raina. Ba wai don na amfana da su bane, e ƙila — tabbas ma na amfana da su — amma kawai saboda kasancewar su kurakurai shi ya sa na ke murmusawa a gare su. Ni ganina nake a cikinsu; ni a mutum ba a halittar da na ƙera wa kaina ba. Ni a gangariyar mutum mai kuskure. Mutum Ajizi. Shi ya sa na ke murmushi, dan a kullum suna tuna mini da waye ni idan na zama mai mantuwa— saboda mantuwa halittace da aka yi ta dan mu. 

Mantuwa na da tasiri ƙwarai a wannan bigire saboda ni dai ba komai na ke iya tunawa ba. Misali ba zan iya tuna ababen da suka faru da na ke shekara 10-15 ba, saidai ƴan kaɗan da ga cikin abubuwan da suka wakana. Na san na yi rashin lafiya a waɗannan shekaru, sannan nuna hazaƙa kwarai a makaranta. Sannan zan ɗan iya tuna abokaina da wasu abubuwan da suka faru da Ni kaina. Waɗannan duk ba su kai kaso 10 cikin ɗari daga ciki ba. Mantuwa na da daɗi. Har fuskoki ma ina mantasu, ina manta yadda duniyata ta kasance a baya, ina manta waɗanda suka munana min da ma waɗanda suka taimaka min na tsallaka titi. Waɗanda suka zage ni da ma waɗanda suka yabe ni. Tabbas mantuwa na da daɗi! 

Akwai kuma gulbin tunani da ke cigaba da ke cigaba da cika kamar a tsakiyar damuna. Zan iya riskar komai a duniya ta hanyar tunani. Ina shagala ƙwarai a wannan yanayi, duk da yake dai; da tunani nake tunanin, amma hakan ba ya hana ni samun cikakkiyar annashuwa a yayin yin sa. Ina farin ciki ƙwarai a wannan dausayin, ina kasancewa tatil tamkar wanda ya kwana a buge tsabar farin ciki. Ko dai tunanin ne ke bugar da ni ko kuma kasancewar na san ina tunanin ne, ba na ce ba. Misali, zan iya tunanin cewa ni ina tunanin abu kaza da kaza sun faru a gare ni, ko na mace ne ko ina raye. Sai kuma na fara tunanin yadda abin ya kaya ko da ina a raye ne ko a mace. Tunanin ba sa damuwa da kasancewa ta a mace, su ko a jikinsu. Kawai za su cigaba da tafiya ne bisa tsarin da ruhina(ƙila) ya tsara. Hakan kuwa na birge ni matuƙa kuma ina samun biyan buƙata— duk da bani bane nake tsara su, zuwa suke. Biyan buƙatar kuwa da nake samu ba ya wuce kasancewar ina iya sanin abin da zai wakana da raina ko babu. Hakan na matuƙar ƙayatar dani. Duk da yake, wasu lokutan, ina jan ragamar tunanin zuwa in da nake so su je— saboda zan iya hakan kuma ina da ikon yi hakan, tunda tunanina ne bana kowa ba. Ina matuƙar son wannan ɓarin na duniyar tunanina. Ban son me yasa ba, amma ina jin, ƙila, saboda ni ne mai yinsu ba kowa ba. 

Hakazalika, duk a nan duniyar, na kan samu kaina a wani yanayin da ke sani tunano duk abubuwan da suka faru, da waɗanda za su faru, da waɗanda nake so su faru, da waɗanda nake fatan su faru, da waɗanda nake hanƙoron faruwar su, da waɗanda haka kurum suke faruwa. Iya wannan na iya kaini duk wani irin bene na farin ciki da ɗan adam zai iya kintatawa. Idan ma kintacen za ya kai can sama-saman-samaniya ne, to ni ma farin ciki na na wurin, tare da.... 

Kada ku bi ta zancena, kawai ina labarta muku kaɗan daga cikin ababen dake shigowa duniyata ne da zaran na ɗaga kayi na ko ruhi na. Da zaran na kaɗaitu, da zaran yanayin shiru ya riske ni. Shi ya sa nake son barci. Amma fa, hakan ba ya hana ni ƙin shiru, saboda a wasu lokutan — a gaskiya, lokuta masu yawa — na kan riski aminci a wannan yanayi. Shi ya sa nake son shiru. Kuma ina son barci. Kuma ma ina son tunani — saboda suma da hular shiru suke zuwa, matayensu kam da kalabinsa, aworworansa, mayafinsa, murmushinsa, kyawunsa. 

Kai ina son shiru, a halin yanzu ma a can wata ƙasa a duniyar tunanina, ina zaune a dandamalin rayuwa ina mai kallonta, a samana akwai bishiyar Ɓaure mai girma da faɗi. A gefe na akwai moɗar shayi. A can gaba na kam akwai kyakkyawar budurwa mai cikakken zati, ni kuwa sai kallonta nake: ina shan shayi, ina ta son shiruna!  


08/05/25
MA. Maibasira

Sunayensu

Eh su, mai sunan su,
A haka aka haife su babu sunayensu?

Lokacin da kuke buƙatar kuriunsu,
Ku ne har mazaɓarsu dan ku tantancesu

Loton nan har hotunan su kuka maka,
A bango saboda kar ya wucesu.

Sai yau ɗin da ba ransu,
Saboda rashin ta ido kuka manta sunayensu?

Ina kuke lokacin da a ka kashe su,
Aka sare su sannan aka ƙona su?

Ina kuke lokacin da suke neman agaji,
Da bakunansu, babu mai kula su?

Ina kuke lokacin da aka ciri ɗaya daga kwata,
Aka wurga shi dan a ƙona su?

Ina kuke lokacin da fatar su yake zagwanyewa,
Ƙuna da raɗaɗin azaba na ta cin su?

Ina kuke lokacin da tsabar azaba,
Ta tayar da gaɓoɓin wasunsu?

Ina kuka ɓoye lokacin da aka fara bin,
Karnukan su da sara a na kashe su?

Ina kuka ɓoye lokacin da suke fitar da,
Hayaki daga bakunansu?

Na ce ku matsiyatan nan, marasa mutuncin nan,Masu ribatar nan, 
Ina kuke lokacin da suka rasa rayinsu?

Yau hawaye ke kwaranya a fuskata,
Zuciyata duk ta cika da raɗaɗi sanadinsu.

Akwai nauyi a ruhina a duk lokacin da na tuna da su,
Ji nake yi tamkar na ma san su.

Ban san sunayen su ba har yanzu ,
Saboda ƴaniskan sunƙi su duba su.

Na dai sanya masu suna,
Akwai Aminu akwai Ilyasu.

Da Ɗalhatu da Haruna,
Ƴan uwan juna na san su.

Ibrahima Halilu, kamili,
Ƙurani da Hadisai yana ta dakon su

Zubairu mai masoyiya zubaida,
Har yau ta kasa kallon bidiyon su.

A kullum hawaye ne ke kwaranya,
Idan har ta tuna da yadda aka ma su.

Sai ta ji kamar ma ana ƙona ta,
Idan ta tuna da soyayyarsu da Alkawarin su.

A zuciyarta wuta ke ta burtsatsowa,
Wutar bege da kewansu.

Shi kenan babu Zubairu,
Ya tafi kenan shi da ma sauransu. 

Na tuna da na cikin tayar nan,
Ɗan farin nan mai suna Harisu.

Na tuna yadda suka masa,
Yana ihu su kuwa suna dariyar su.

Ya na ta ajiyar zuciya,
Su kuwa suna ta muguntarsu.

A duk lokacin nan babu ɗaya daga cikin—
Su ƴan iskan nan da ya zo agajinsu.

Haka aka yi ta yi tsawon awanni,
Mutane fa a ƙasarsu.

Aka yi ta ƙona su ana daɓe su,
Da su da muradansu;

Abubuwan da suka so suyi,
Abubuwan ma da suke kan yi nasu.

Da masu ajiye kuɗi a cikin jaka,
Da masu ajiye shi a asusu.

Kudaɗen da za su saya wa,
Masoyansu balangu da kilishi da su.

Kayan sallah kuwa an tura kuɗi,
Yana nan yana jiransu.

Su zo su sanya sa,
Ashe babu damar ya gan su.

Iyayen da ke tagumi duk yamma,
Saboda kewar rashin ɗansu.

Ƴaƴayen da ke zaune a ƙofa,
Suna ta dakon dawawar ubansu.

Ashe ya tafi kenan,
Sai dai gawarsa za a kawo masu.

Ruhiƙa sun ƙunana,
Zuciyoyi ma da rauninsu.

A kullum da shi za su tashi,
Da safiya har zuwa barcin su.

Ƙunar rashi madauwamiya,
A kullum suna ta dakon su.

Ba fa ma rashin ba ne kaɗai,
Har da ma yadda aka zo gunsu —

Da labarin yadda,
aka daddatse jininsu.

Aka bige su, aka ƙona su,
Aka raunata su.

Akwai ƙunci da ɗacin,
Da ke daskare a wani saƙo nasu.

Haka za suyi ta dakon su,
Har ƙarshen rayuwarsu.

Mafarkai da burikan masoyansu,
Na can ƙuryar ruhikansu.

Soyayya da ƙunar rashin masoyansu,
Saboda tsabagen wauta ta mutanen ƙasarsu.

Wautar da ƴaniskan suke rurawa,
Domin biyan buƙata nasu.

Tashin tashina za ta cigaba da ɗorewa,
Har sai sun shiga taitaiyinsu.

Idan suka ƙi shiga ta lalama,
Ai sai a koya masu.

Ta hanyar fitar da su,
daga ɗakin da suke, su je can masu.

Mu koresu, 
Mu yi fatali da kayan su.

Mu ƙi yarda da duk batun su,
Ko ma wani abu da zai fito daga bakunansu.

Mu tsaya da kafar mu,
Wajen yin ball da su.

Tun da sun iya rura wutar kabilanci,
Mu Kore su, mu kakkaɓe tabarmarsu.

Mu faɗa masu ba su da matsuguni a nan,
Su tashi su yi tafiyar su.

Mu faɗa masu ƙasar ta mu,
Ba ta zamowa filin wasansu.

Da zasu dinga amfani damu,
Wajen biyan buƙatarsu.

Mu tuna masu da dubunnai,
Da aka salwantar da ransu.

Mu tuna masu da masoya biyun nan,
Da aka raba su har da soyayyarsu.

Mu tuna masu da hawayen mahaifiyar nan,
Da tagumin ƴaƴayansu.

Mu tuna masu da kwantacciyar ciwon nan,
Da ke binne a zuciyar ahalinsu.

Mu tuna masu da zaluncinsu,
Da ke rura wutar ƙiyayya duk domin su.

Mu tuna masu da soyayyar da ba a kai ga cimmawa ba,
Ƙaunar da aka rusa wa wasunsu.

Mu tuna masu da komai,
Komai har da furfurar wasunsu.

Kar mu bar su,
Kar mu sake su.

Idan suna guduwa,
Mu taɗe su, mu ingiza su!

Su rasa sukuni a yankin su,
Har sai sun tuna da sunayensu.

Da Kuma Akwai Wannan Lumanar Da Ba Za A Iya Fasalta Wa Ba

Da akwai wannan lumanar da bawa kan riska yayin da ya tsinci wannan littafin da ya yi shekaru yana nema a wata ƙurya a cikin ma'adanar t...