Saturday, 1 November 2025

Tsakanin Haske da Duhu


Lokaci kaɗan sai hasken makomar wannan ƙasa ya baɗe mini ɗakina. Lokaci guda kuma sai ya janye, ya daina kwaranya a dausayina. Ƙasar nan tamu ce, ita kaɗai ce gare mu, amma a yau na kasa shaida ta; na kasa gane kalar mayafinta. Wasu daga cikin ƴaƴanta na dunkule shara a hannu, su watsa ai ta rububinta. Su damtse mana yatsu, su mika mana azurfa mu yi ta yabonsu. Yau sukuni ya yi ɓatan dabo a sarari ya koma can inda rana ta kwanta. Yau babu mai kallon kwanciyar rana ballantana ma ya yi tunanin sukuninsa — da ke can tare da rana, yana dakon komowar sa. 
Haske yakan tuna mini da ƙauna, duhu kuma ya kusanto ni ga wutarta. Haske da duhu na tasaruffi a zuciya, su suka turniƙe sararinta. Yaushe za mu samu sukuni a can sadarin rana to? Yaushe duk abubban za su rikiɗe ya zam hadarin ya kau? Yaushe ruwan za shi sauko; ƙasa ta fid da ƴaƴanta? Ƴaƴaye kyawawa masu yabanyar zaman lafiya. Yaushe ne makomarmu za ta haska ta bayyana mana da lambunta? Da ke ɗauke da shukoki iri-iri masu kalar lumana? 
Ƙasar nan da zafi da ƙunci. Sannan an ƙi ba mu mafaici. Idan muka je nema sai fa maɗaci. An damƙe mu an barmu da ƙirci. Ƙasar nan da ƙuna a ƙalbi, ƴaƴanta ba su da sukuni, zuciyoyin kowanensu da rauni, da ke shiga har cikin rai yai mulki. 
Bishiyar Gamjin ta fara mutuwa, rassanta na ta bushewa. Mikiyoyin na ta rage yawa. Zakunan ga su a na ta bindigewa. Taurari mahaskaka suna ta rage yawa. Hayaƙin ƙunci a ko'ina na turniƙewa. Amma, har yanzu, rana na fitowa: hadari na haɗuwa, iskar hunturu na kaɗawa, yayyafi na saukowa (a hankali amma).
Duk da yake kududdufin ya kusa bushewa, rijiyar na ci gaba da cika da batsewa. Duk da yake hasken na janyewa, akwai ranar da za ta kuma dawowa. Duk da yake malam-buɗe-littafi na ta ɓacewa, akwai tsuntsayen da ke shilgawa. Duk da yake gangar ta kuma fashewa, kiɗar na fa canza wa. Duk da yake duk abubban da nake ta faɗa hasashe ne, ba a raba ɗan Adam da wassafawa! Saboda ƙasar nan dai ita kaɗai gare mu, ba mu iya sauyawa. Saboda ƙamshin turarenta a jikkunanmu ba shi taɓa nasuwa. Saboda bugun zuciyarmu na tafiya ne a bisa tsarin wannan uwa. Saboda a duk sanda muka tsinci kanmu a rana ita ce ke zame mana inuwa. Saboda ko ina aka binne mu, ƙarshe ruhinmu shigifarta zai kuma dawowa. Saboda ita ce mafari kuma ita ce kushewa! Saboda ko ina za mu, alƙiblarmu na a gidan wannan tauraruwa. 
Idan muka ɓace a saharar rayuwa, ita ce za ta nuna mana hanya mafi karɓuwa. Idan muka gaza samun ruwa a saharar, ita ce za ta zo ta yi mana ban ruwa. Ita ce mafakar matafiyi idan ya ya yi nitso a ƙangin damuwa. Ita ce mai ceton sa idan ya dulmiye ya kasa fitowa. Wannan ƙasa ce komai, kun ga dole matafiyi ya ci gaba da tarairayar wannan uwa. 
Haske za ya iya dawowa, duhun zai iya yayewa — tamkar giza-gizan da hannu ba ya iya taɓowa, tamkar murjanan kalmomin da ke da daɗin furtawa, tamkar sanyayyar iskar asubahin da ke sanya annashuwa. Tamkar... Tamkar... Tamkar ita. Ita ɗin dai wannan uwa!
Alhassan Maibasira 
11/08/25

Thursday, 9 October 2025

Idan Na Zamo Darbar Fure, Shin Za Ki Iya Zama Filfilon So?


Ita zatiyyar so idan ta yi nasarar bayyana haskenta ga masoya ance sukan rikice. Wasu ma sukan makance. Wasu kuma sukan zamo darbar fure da filfilo. Shin idan na zamo darbar fure za ki iya zama filfilon so? Sai dai rayina ba zai so a ce kina sauka a furanni kala-kala ba. Rayina zai so a ce a guna kaɗai za ki tsaya. Kamar dai filfilolin da kan sauya kalolin fukafukansu saboda tasirin furanni da ganyayyakin da ke gudanuwa a rayuwarsu. Ni ma, haka na ke so na zamo gare ki.

Amma kuma, darbar da ke ɗauke da sinadarin so na iya bugarwa ai, ban son ki soma layi a saman iska ki faɗa hannun gizo da ƙoƙi su yi kalaci da ke. Ko kuma ki fara rausayawa ƙarshe ki rikiɗe ki dawo bil'adama ni kuma na ci gaba da zama a ke. Ni zan iya jurar haka na tsawon zamani. Ke fa? Filfilo kan bayyanar da irin ƙaunar da ke a kushewa marar lamba a zuciya. Filfilo kan haske hasken ƙauna a dausayin masoya. Yakan sanya walƙiya ta bayyana a duhun idaniya. Shafukan ƙauna kan buɗu a duk lokacin da fukafukinsa ya kaɗa...

Ko dai mu zama filfilolin ne a tare? 

Ni da ke, filfiloli biyu a sararin sama. Mu tanɗo manɗon darbobin ƙauna mu tanɗa wa junanmu. Ƙarshe dai zafin so ya narkar da mu, mu rikiɗe mu zamo darbobin so. Sai mu ci gaba da ƙawatar da duniya da mazaunansa masu tafiya da saƙar zumar ƙauna a rataye a wuya!

Alhassan Maibasira 
09/10/25

Thursday, 11 September 2025

Jariran Taurari


So samu, a samu malam-buɗe-littafi; kore mai zanen jariran taurari, ya taimaka ya buɗe mana shafukan rayuwa — ko rayuwa ta yi haske. Ga ki sanye da riga koriya, ga shi da fuka-fuki mai walƙiya. Ga ki mai zubin yaƙutiya, ga shi mai buɗe ƙofar hasken zuciya. Zo mu buɗe shafukan so da ƙauna. Zo mu wilkita mu biyu a samaniya.

Mu rikiɗe mu yi ta tsalle a saman itaciya. Mu tsaga, mu fasa, mu tanɗa wa junanmu zaƙiya. Mu yi waƙa irin ta zabiya, ta gwauraye duk ko'ina a nahiya. Mu ƙone fuka-fuki a lokaci ɗaya, mu narke mu wuce samaniya.

Idan muka ƙare sai mu dawo duniya, ni a fure ke a ranata - tauraruwa. Ki haska mini hasken ƙauna, na buɗe zuciya domin na samu karɓuwa. Ki ƙawata mini duniya, na kasance mai miki addu'a zinariya: “na gode na gode sarauniya; kin cire mini duhu, kin ƙawata duniya.”

Idan lokaci ya yi sai mu dawo a bil'adama. Mu yi rayuwa irin ta sarki da sarauniya. Mu samu malam-buɗe-littafi guda ɗari ba ɗaya, domin su ci gaba da ƙawatar mana da duniya. 

Tunda labarinmu ba ya taɓa sabkuwa. Tunda soyayyarmu ba ta taɓa nasuwa. Tunda ƙauna ba ta da ranar ƙarewa, tunda a wannan fagen babu batun rabuwa, tunda akurkin ba ya taɓa zama kushewa, to ai kin ga dole mu ci gaba da rayuwa!

Ke ɗin mai riga koriya, maƙwaƙwafar da ke tono zumar ƙauna. Ke ɗin mai daɗaɗa dausayin zuciya, walƙiyar da ke gilma wa a samaniya!

10/08/25

Wednesday, 16 July 2025

Da Kuma Akwai Wannan Lumanar Da Ba Za A Iya Fasalta Wa Ba


Da akwai wannan lumanar da bawa kan riska yayin da ya tsinci wannan littafin da ya yi shekaru yana nema a wata ƙurya a cikin ma'adanar taliffai. Duk yadda wannan bawan zai yi kuwa, ba zai iya sa ta a gurbin da ya dace da ita ba.

Ko da zai ce: ya ji wani abu a cikinsa tamkar an kuma haihuwarsa. Ko kuwa: zuciyarsa ta fid da fuka-fuki ta lula samani inda ta zauna tare da rana har ta narke. Ta gwauraye da iska. Ta zama marar nauyi. Ta tsaya cak. Ta yi ta ruri, gunji, tana neman mafari. Ko da zai ce: ya kasance tamkar lokacin da aka halicce sa — kafin a sanya so a cikinsa; kafin ransa ya samu hankali. Wannan lumanar da ya riska tsakanin hankali da rashin hankali. 

Ko: ya ji kamar ya mutu baicin yana raye; kamar duniya kowa ya mutu sai shi kaɗai; kamar a samaniyar ma babu giza-gizai; kamar farin cikin mahaifiyarsa lokacin da ya fara kiranta da ‘Mama’; kamar irin walƙiyar da ya bayyana a idaniyarta a san da ya fara ta-ta-ta. Irin tagomashin da ke wanzuwa yayin kallon fuskar masoyiya. Irin yabanyar da ke fitowa daga ƙalbi a yayin kallon murmushin masoyiya. Irin macewar da rai ke yi a lokacin da ya ji ƙamshin turaren masoyiya.

Ko ko ma: ya ji tamkar matalaucin da ya riske alatu a kogo, ko kuwa ma mai karayar arziƙin da arzuƙansa suka dawo. In ya so ya ce: ya ji kamar yaron da ya soma ɗanɗanar romon ilimi: garɗin sa, zaƙin sa, mai yawan sukari. Annashuwar da ke ɗarsuwa a rai idan ya amsa tambaya daidai; Iskar da ke wantagaliliya da kafatanin tunaninsa a yayin da ake tafa mai; rijiyar shauƙin da ke ta amayar da wuta a maimaikon ruwa; yanayin da ya tsinci kansa a lokacin da rayuwa ta lasa masa zauƙin da ke a miyar ilimai.

Duk waɗannan ba za su bayyana iya girman yanayin da ya shiga ba. Duk waɗannan ba za su haska wa makaranci iya tumbatsar da ɗan ƙaramin dunkulen da ke a ƙirjin bawan nan ke yi ba. Duk waɗannan sai dai su kwatanta wa mai karatu iya budum-budumar da bawan nan ya yi a cikin kogin farin ciki.

Kuma ya tsinci kansa a wannan yanayin ne a wata ƙurya, wadda haske bai wadata ta ba, wadda ƙura ce ke ƙawata ta, wadda aka daɗe ba a leƙa ta ba. A can wani ɗan ƙaramin ɗaki mai ɗauke da tulin litattafai.

08/07/25

Wednesday, 2 July 2025

Sihirtacciyar Salka


Akwai wasu halittu da ke nasarar killace rai a matsayin ruwa su sa shi a salkarsu. Su ba sha za su yi ba, ba kuma fito da ran za su yi ba har sai sun kai madakatarsu. Sai su zubar da ruwan walau a ƙasa ko a cikin randar gidansu. Idan ya ci sa'a suka saka shi a randar, to ba ƙaramin farin ciki zai yi ba, saboda ko ba komai: zai sirku da ruwan gidansu, za su tsotsa daga sinadaransa, zai kuma dinga jin sautin muryarsu, da ma ƙamshin turaren su. Zai kuma shige can cikinsu. Zai iya tagomashi da sirrikan da ke kwance a cikinsu.

Idan kuma watsar da ruwan suka yi a ƙasa, sai ya yi ta ratsa yashi da tsakwankwani; tsutsosi da ƙananun halittu; aljanu har ma da ɓurɓusan ƙasussan bil'adama da dabobbi; ƙasashen zamanin da da ƙasa ya rufe; kududdufai da ma’adanar kayayyakin alatu; har ya isa inda zai haɗu da sauran rayuka kamar sa, inda suke zaune a daira, ƙafafun kowannensu a tankwashe. Suna masu karatu daga wani littafi — mai kama da littafin so.

Abin mamaki kuwa, duk cikinsu, babu wanda ya san sunan halittar da ya haɗu da. Babu wanda ya damu ya san sunanta. Kawai makillaciyar ransu ce suke so, ita ɗin da ba ta da suna.

Su kuma waɗannan halittun ba su ma san da sun yi hakan ba. Ƙila murmushi suka yi kawai, ba su san da cewa a take rai ya narke ba; saboda zafin wannan murmushin a gare sa. Saboda tsananin farin cikin tozali da wushiryar makillaciyar ransa. 

Ƙila kuma kallon sa suka yi da waɗannan idaniyar ta su, wandararru, masu kama da rana a tsakiyar sahara, sai ransa ya fara amon wutar ƙaunar wannan idaniya; ya kasance mai fata ya zama ko da ruwan idaniyar ne — sai kuma ya zama! Amma maimakon ya ƙare a idanunta sai ya gan shi a salkarta. Amma kuma ita ke riƙe da shi a hannunta. Hakan ya wadatu a gare sa!

Ƙila kuma kiran sunansa ta yi, sai kawai ya ga ransa ya fara fiddo da fuka-fukai. Ransa ya zama kamar wani mala'ika. Ya yi ta harbawa sama har ya cimma zara ya zauna a bisanta. Sai ya narke. Sai ya zamo ruwa. Ya sulalo daga sama ya shige cikin salkarta.

Akwai wasu halittun da ke ƙona rai, su narkar da rai, su zuzuta rai, su haukatar da rai, su kuma makantar da rai. Yadda suke so — duk da yake ba lallai da sonsu ba, amma shi rai bai damu da wannan ba.

Akwai waɗannan halittun a ko'ina. Kuma a koyaushe idan na haɗu da su, sai na zame ɗaya daga cikin nau'kan ruwan salkarsu. 


17/06/25

Saturday, 14 June 2025

Matafiyan Tsuntsaye


Akwai mutanen da suka kasance kamar tsuntsaye matafiya; sukan shigo rayuwar mutum lokaci guda — na lokaci ƙalilan. Kamar matafiyan tsuntsaye, sukan yi sheƙarsu a rayuwar mutum su yi ta rera masa waƙoƙi — su warkar da ciwukan zuciyar da ya addabe sa, su gyara masa rayuwarsa. Abubuwan da ba ya yi sai ya fara; idan ya faɗi su tayar da shi, idan ya kuskura hanya su dawo da shi bisa tafarki, idan ya nemi shagala su watsa masa ruwa don ya tashi. Idan ya nemi ya ɓata, su nuna masa hanya, duk ta hanyar waƙoƙinsu, waɗanda suke rerawa a kodayaushe. 

Kamar matafiyin tsuntsu, sai ya yi tafiyarsa ya bar sheƙar a saman bishiyar. Babu kowa dai a kai, amma a duk lokacin da mutum ya ɗaga kansa sama, zai hango gidan wannan tsuntsun da ya sauya masa rayuwa. Ba lallai ya kuma dawowa ba, ya tafi kenan. 

To haka Malam Jamilu ya zame wa rayuwata. A daidai lokacin da na gaza gane ina na dosa, sai ya yada zango a bisa bishiyata, ya yi ta rera mini waƙoƙin adabi, tarihi, da wasullan Hausa. Ya yi ta ciyar dani daga tsirran ƙasar Hausa. Idan na kishingiɗa ya taso ni, yace mini na je na nemo masa ciyayi domin mu tada baƙi. Neman ciyayi kam dama na bani wuya, amma duk da haka bai saduda ba. Akwai fa bishiyu da dama a wannan jejin, amma ni kaɗai ya horar fiye da misali. Ni kaɗai nake jin haka — kusan kowa yana sauraren waƙoƙinsa kuma yakan aike su domin su nemo ciyayin. 

A lokaci ƙalilan, bishiyata ta fara rassa, da kaɗan, da kaɗan furarruka suka fara fitowa. Sai dai an ɗau tsawon lokaci kafin bishiyar ta fara ƴaƴa. Lokacin ya bar shingen mu. Idan ma yana dajin baya kusa damu. Ni kuma saboda wautata sai na mance da shi, na ƙi na biɗesa. Na ƙi na tambayi ƙwari da tsutsosin da ke ƙarƙashin ƙasa ko sun taɓa ganinsa. 

Yau dai bishiyar ta fara ƴaƴa — haka nake tunani. To saidai, ashe ba zai taɓa riskar ƴar bishiyar da ya raina ba da kansa. Yar bishiyata da ya rera wa waƙe, ƴar bishiyar da ya zame wa fitila a cikin duhun dare. Yau ba zai gansu ba, yau ba zai taɓa dawowa bisansu ba. Ya tafi kenan, ashe ba zai kuma dawowa ba. 

Akwai mutanen da suka kasance kamar matafiyan tsuntsaye: sai su haskaka alƙaryar mutane da zatinsu, su yi ta shawagi a bisansu, su ƙayatar da duniyarsu. Sai kuma su tafi, za su dawo? Ƙila.... Wasunsu kuma sun tafi kenan. Sheƙarsu na nan dai, hakana tasirin su ga rayuwar mutanen alƙaryar. 

Irin waɗannan mutane ba sa mutuwa, ko sun mutu da akwai ɓurɓushinsu a jikin kowanne. Da akwai baitukan waƙoƙinsu a dashe a ƙalbin mutane. Da akwai ƙarin harshensu a bakunan mutane. Da akwai garɗin koyarwarsu a dasashi da ma saiwar bishiyoyi. Kogunan alƙaryar kam za su ci gaba da ɗaukar wasulla da baƙaken da suka taɓa suɗaɗowa daga waƙoƙinsu. Irin waɗannan mutane na rayuwa har abada. Irin waɗannan mutane ba sa mutuwa.

Allāh Ka gafarta wa bawanKa; Ya kasance kamar matafiyin tsuntsu ne a ban ƙasa. Kai ne Majiɓincinmu, Kai ne Mai rahama a garemu. RahamarKa ta baɗe ko'ina. RahamarKa na da tasiri akan kowa. Ka sanyaya masa yadda ya sanyaya mana. Ya yi iya nasa ƙoƙarin wajen kula da bayinKa; wajen ciyar da halittarKa; wajen ɗanɗana wa al'ummarKa daga ilimin da Ka tsam masa; Ka sa ya zama mai ƙwanƙwaɗa daga tafkin rahamarKa, don, koda ƴar ɗigo ya samu, ta wadace shi har abada. Allāh Ka gafarta wa Malam Jamilu, mutum ne salihu da bai son fitnu, ka buɗe masa ƙofofin rahamarKa, domin, ya kasance mutum ne mai kyawawan ɗabi'u.

Marigayi Malam Jamilu (d. June 2025)



Monday, 9 June 2025

Yawon Duniya

Masoyiya, shin za ki iya shimfiɗa 
Mini tabarma a wani sashe na 
Zuciyar ki don na zamna?
 
Ƙafufuwana sun gaji da 
Taku a cikin zuciyarki 
Babu dare, babu rana.

Ba lallai sai kin samo 
Kilishi ba ko kujerar 
Nan mai taushi da laushi.

Kawai soyayyarki nake so 
Ta zame mana tabarma; 
Ni a gefe ɗaya, ke a ɗaya.

Ta ja mu, ta ɗaga mu, ta lula mu:
Mu keta gajimare; mu ratsa ta 
Gangamin tattabaru; mu wuce sinadaran
Numfashi; mu lula mu tafi can inda cida 
Ke koyan tashi. Daga nan, ƙila, 
Sai mu garzaya duniyar taurari;
Mu faɗa kogin da ke bisansu, mui wanka, 
Mu sauya buƙatu, mu kaifafa muradai;
Mu tsaftace soyayyarmu.

A cikin zuciyarki, da zaki yarda, 
Da sai na janyo tabarmar nan bakin teku. 
Mu zamana muna kallon shirgawar 
Kifaye mu kadanmu 
Sai kuma teku.

Da zaki yarda, da sai na baza 
Komata don na kamo kifayen 
Da ke cikinai, kowannensu, na 
Buɗe cikinsu, inda ƙoƙon lu'ulu'u 
Mai ɗauke da soyayyarmu 
Ke ciki a ɓoye.

Masoyiya, so nake kawai na samu 
Aminci a cikin zuciyarki; ki ɗan lasa 
Mini daga tekun ƙaunarki; ki ci gaba 
Da alkinta mana soyayyarmu a cikin 
Ƙokon lu'ulu'u nan mai haske. 
Ƙila wataran, idan muka ƙare 
Yawon duniyar mu, zamu shiga 
Domin mu ga iya girmanta. 

Fatana

  Fatana shi ne a ce, ga ni, ga ki, ni da ke, a cikin madafa muna haɗa shayi. Ki ɗan tsoma ganyen na'a-na’a, ni kuma sai na ɗan watsa ka...